NUJ Kaduna Na Jimamin Rasuwar Mahaifin Tsohon Shugaban Kungiyar Adamu Yusuf

0
290

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

CIBIYAR kungiyar ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan tsohon shugaban Kungiyar, Alhaji Adamu Yusuf bisa babban rashin da suka yi na rasuwar mahaifinsu wanda ya faru a jiya Alhamis 31 ga Maris, 2022 a Kaduna.

A cikin sakon ta’aziyyar, shugabar Kungiyar ta Jaha, Asma’u yawo Halilu ta yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, Yasa Aljannah Firdausi Makomarsa da iyalansa baki daya, kana da addu’ar fatan Allah ya basu ikon jure wannan rashi mara misaltuwa.

Hakazalika, a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren Kungiyar, Gambo Santos Sanga, ya bayyana cewa rasuwar mahaifin Alhaji Adamu Yusuf daga wannan duniyar mai cike da zunubai wani al’amari ne daga Ubangiji, ganin cewa lamarin ya faru ne a cikin sa’o’i arba’in da takwas da ake gab da fara azumin watan Ramadan na wannan shekarar.

Allah ya jikan mahaifin namu da rahama.

Leave a Reply