Sojoji Za Su Koyar Da ‘Yan Jaridun Kaduna Salon Makamar Aiki Da Al’adun Soji

0
420

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KWAMANDAN Cibiyar jagoranci da zaman lafiya ta Martin Luther Agwai, Jaji, Manjo Janar Muhammad Fagge, ya bayyana shirin horas da ‘yan Jaridun Kaduna kan ilimin sanin makamar aiki da al’adun soja domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin Jama’a da soja.

Hakan dai ya zo ne kamar yadda Kwamandan ya bukaci ‘yan jarida da su karfafa wa mazajen da ke sanye da kayan aikin kwarin gwiwa ta hanyar rahotonsu.

Fagge, ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), reshen Jihar Kaduna a yayin ziyarar ban girma da suka kai cibiyar kasar.

Ya kuma jaddada bukatar hadin kai da hadin gwiwa tsakanin jami’an soji da ‘yan jarida, yana mai cewa ya kamata hukumomin biyu su yi aiki tukuru wajen ciyar da al’umma gaba, ci gaba mai inganci.

“Abin farin ciki ne na tarbe ku a yau domin kara karfafa daddadar dadadden zumuncin da ke tsakaninmu a matsayin abokan hulda, wajen gina kasa mai zaman lafiya da karfi.

“Ba za a iya bayyana rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen ci gaban kasa domin cimma burinsu da burin iyayenmu da suka kafa mu ba.

“Za mu ci gaba da dorewar dangantakar da ke tsakanin cibiyoyinmu don amfanin babbar kasarmu .

“Kamar yadda ku ke gani da kanku, wannan cibiya tana dauke da kayan aikin fasaha da aka gina ta hanyar fasahar zamani domin sanya ilimi da da’a ga sojojinmu da ke aikin wanzar da zaman lafiya,” in ji Fagge.

Tun da farko, shugabar kungiyar ta NUJ, Kwamared Asma’u Yawo Halilu, ta bayyana shirye-shiryen shugabancin Kungiyar tare da karawa ‘yan jaridun sama da 400 kwarin gwiwa da sojoji domin amfanin al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here