Connect with us

Tattaunawa

Na Yi Aikin Biliyoyin Naira A Mazaba Ta – Ibrahim Mustapha Aliyu

Published

on

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

HONARABUL Ibrahim Mustapha Aliyu, dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Raba da Wurno daga Jihar Sakkwato wanda ya kasance mataimakin shugaban kwamitin tsara birane da yan kuna a majalisar wakilai ta kasa ya bayyana cewa ya yi wa mazabarsa aikin raya kasa da kudin da suka kai sama da naira biliyan daya a yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.

Ga dai yadda hirar ta kasance

GTK: Shin mene ne ribar da al’ummar mazabar ka suka amfana da shi daga gare ka a matsayin wakilinsu?

Hon Ibrahim: wato duk da cewa aikin dan majalisa shi ne yin doka da kuma zuwa aikin zagayen sanya idanu domin ganin aikin da aka yi da kudin da aka ware don yin aikin wanda majalisa ta amince da su, nayi iya bakin kokarina kuma ina kan yi ban fasa ba.

Saboda irin yadda na san hakkin da ya rataye a wuya na ban yi kasa a gwiwa ba, sai da na yi kokarin sama wa mazaba ta ayyukan raya kasa, koda yake ni a wuri na abu ne da har ma na mance da shi misali daga titin marabar Raba zuwa marabar Bakura da aka yi shi a tsawon shekaru Talatin da hudu da suka gabata kuma ya lalace kwarai ga kuma al’ummar wannan wuri na cikin matsalar rashin hanya, wato matsalar samun sahihiyar hanyar daukar kayansu musamman na amfanin Gona ya zama masu wahala kwarai.

Don haka na ga cewa lokaci ya yi da zan rungumi wannan lamarin aikin hanya sai kawai na gabatar da kudiri a gaban majalisar wakilai ta kasa kan a gina wannan hanyar kuma na yi ta bibiyar lamarin, ina farin cikin shaida maku cewa a yanzu an kusa kammala aikin wannan hanya abin da ya rage kawai bai fi yan gyare-gyare ba sai a kammala ainihin gundarin aikin a shekarar 2023. Ina jin a halin yanzu aikin zai kai kudi daga miliyan dari Takwas zuwa naira biliyan daya da Digo biyu (1.2b) kuma tsawon hanyar ya kai kilomita Tamanin da daya (81).

Na kuma samu nasarar samun aikin gyaran matsalar zaizayar kasa a wurare shida (6) Wurno, Raba, Marnuna, Rara, Gidan Buwai da garin Achida da aikin zai lashe kudi sama da biliyan biyar da miliyan dari shida (560b) ayyukan kuma sun hada da gyaran wuraren hanyoyi magudanan ruwa da wuraren da suka zaizaye har ma da kwalbatai da duk wuraren da ke bukatar ayi gyara sakamakon matsalar da aka samu ta zaizayawar kasa.

Sai kuma a bangaren batun ilimi, mun samu nasarar samun aikin gina Ajujuwan makarantun Firamare da a halin yanzu an samu nasarar gina sama da guda Bakwai mun kuma samu nasarar yin aikin tituna a Rara, Yar tsakuwa, Gidan Bango kuma mun gyara fadar Hakimi.

Kuma mun yi aiki sosai a bangaren batun rage radadin talauci mun samu raba wa jama’a Babura, Kekunan Dinki, Injunan Saka domin karfafa wa mata su dogara da kawunansu.

Sai kuma bayar da Injunan banruwa ga manoma kasancewar mazabata kusan duk manoma ne don haka abin da kawai zaka yi shi ne ka taimaka masu su samu yin aikin Noma mai yawa.

Akwai kuma ayyukan hadin Gwiwa na mazabu a bangaren makarantu da suka hada da taimakawa dalibai.

Irin kudin tallafin karatun da muke ba dalibai da suke karatu a manyan makarantu da kuma bayar da tallafi domin yin jarabawar JAMB tare da yi masu aikin horaswa a kan yadda za su samu damar rubuta jarabawar cikin sauki bayan sun samu makamar aiki.

Da akwai kuma wadansu shirye-shiryen da dama domin inganta rayuwar mutanen mazabar da nake yi wa wakilci a majalisa. Sai kuma aikin samar da wutar lantarki daga Tofa zuwa Bomawa masaga da ya hada a kalla manya manyan garuruwa shida da suka hada da Raban Maba, Gawakuke, Gidan Almajiri, Burmawar Masaga, Burmawar liman da Gidan Doka ana nan ana gudanar da aikin, kana da akwai kuma wani aikin samar da wutar lantarki a Tunga da tuni har an kammala aikin da dai wasu da yawa da ba zan iya tunawa ba domin hakika mun yi aiki sosai da yawa don haka muke yin godiya ga Allah da ya ba mu damar aiwatar da aikin.

GTK: Kasancewar yankin mazabarka na daga cikin wuraren da ke fama da matsalar yan Ta’adda da sace sacen mutane, a matsayinka na dan majalisa shin wane kira kake da shi game da hakan?

Hon Ibrahim Mustapha: Ni hakika bayani na a nan shi ne a kula domin abin nan ya yi yawa domin akwai wani lokacin da yan bindigar nan suka je garin Raba suka sace wani Jami’in kula da kiwon lafiya kuma suka sace Dabbobi da yawa da akwai kuma irin wadannan matsalolin da ake samu a kusan kullum.

Wato matsalar shi ne mafi yawan abubuwan da muke aiwatarwa da ci gaban jama’a za su iya samun matsala sakamakon irin wannan, amma duk da hakan ina bayar da tabbacin cewa mu na daukar kwararan matakai na kwarai, wasu daga cikin masu wannan aikin an san su da wadanda suke hada kai da su don haka muke rokonsu domin Allah su canza zuciyarsu saboda su sani cewa za su yi wa Allah bayanin komai a ranar gobe.

Kuma a matsayinsu na mutane ya dace ya zama su na da tunanin dan Adam ta yadda suke sanya rayuwar Jama’a cikin matsala su na kashewa, Fade, satar dukiyar Jama’a da sauran ayyukan ta’addanci da dama ta yaya za su yi Karko su na aikata irin wannan aikin Ta’addanci da suka zagaye kawunansu da shi, duk da cewa kowa ya san kwanakinsa kididdigaggu ne don haka dole ne wata rana za ta zo saboda haka muke kiransu domin Allah su canza halin su a samu zaman lafiya.

GTK: Ko akwai gamsuwa game da matakan da ake dauka?

Hon Ibrahim Mustapha: Ba zance na amince ba kuma babu wata hujjar da zance a’a ba, na dai san Jami’an tsaron na yin iya bakin kokarinsu domin yin abin da ya dace sai dai kawai ana samun kalubale kawai.

Duk da batun tattalin arzikin da ake fuskanta mun san shugaban kasa na yin iya bakin kokarinsa kuma ya ba harkar tsaro kulawa sosai, amma dai a kara kokarin sosai.

Ko a kwanan nan sai da na gabatar da wani kudiri a gaban majalisa game da batun yan ta’addan din nan wanda sakamakon hakan duk majalisar ta amince cewa shugaban sojojin Najeriya ya hanzarta samar da sojoji da kayan aiki zuwa Raba da Wurno da kuma samar da sansanin sojoji a Gandi da mahadar Rara zuwa Bulla da Wurno.

Sai kuma shugaban na sojoji ya samar da wurin da sojan za su rika yin aiki daga Munki saboda a baki dayan yankin Sakkwato ta Arewa babu wani sansanin sojoji, da hakan ina bayar da tabbacin cewa an samu kai wa Jama’a daukin gaggawa ga duk inda ake bukatar hakan a samu ceton rayuka da dukiyar Jama’a.

Kuma tun daga kan mai bayar da shawara a kan harkar tsaro, babban sifeton yan Sanda, Jami’an tsaron DSS da dukkan hukumomin tsaro mun yi kira a gare su da su kai jami’ansu wadannan wuraren domin a samu tattara bayanan sirri cikin sauki a samar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

NTA Hausa za ta tattauna da shugaban jaridar Neptune, Dr. Hassan Gimba

Published

on

NTA Hausa Channel 165 a dandamalin Startimes DTT da dikoda Arabsat/Nilesat za ta kawo maku shirin “Bakin Zare” kai tsaye tare da Dr. Hassan Gimba Shugaban Kamfanin Jaridar Neptune Prime.

Dr. Hassan shahararren marubuci, ɗan jarida kuma ƙwarrare mai sharhi kan al’amurran yau da kullum.

Rana: Alhamis, 28th December 2023

Lokaci: 8.00pm

Zamu yi bitar shekara ta 2023 da sharhi kan mahimman abubuwan da suka faru a shekarar.

Ku kasance tare da mu, don jin yadda tattaunawan zata kasance.

Continue Reading

Kasuwanci

Menene manhajar ‘Kapo drive’?

Published

on

Wanda ya ƙirƙira manhajar ‘Kapo drive’ ya ziyarci ofishin jaridar Neptune Prime dake Abuja, inda ya gana da shugaban Neptune Prime, Dr. Hassan Gimba.

Neptune Hausa ta tattauna da ya ƙirƙiro manhajar ‘Kapo drive’, ga yadda tattaunawan ta kasance:

Neptune Hausa – Tarihin rayuwar ka

Muktar – Sunana Muktar Auwal, an haife ni a jihar Yobe, shekaruna 26. Nayi firamare da sakandare a garin Abuja da jihar Kano, nayi jami’ar El-Razi dake ƙasar Sudan, na karanci Ilimin Kasuwanci da Ilimin Lissafin Kuɗi.

Neptune Hausa – Menene manhajar Kapo drive?

Muktar – Manhaja ce da za ta sauƙaƙa tafiye-tafiye, da kuma farashi mai rahusa. Kuma muna so mu ga mun zarce sauran manhajar tafiye-tafiye, wanda ba na ƙasan nan bane, suna kuma chaji kashi 25 cikin 100, wannan ‘Kapo drive’ in na ɗan ƙasa ne kuma muna chaji kashi 10 cikin 100. Za mu rage matasa masu zaman banza, da samar musu da abin yi.

Neptune Hausa – Manhajar a duk Najeriya ce ta ke aiki?

Muktar – A yanzu a jihohi biyu ne, garin Abuja da jihar Kano. Amma muna sa ran a wasu jihohin nan ba da jimawa ba.

Neptune Hausa – Yanzu kamar motoci nawa kuke da su?

Muktar – Muna da motoci ɗari a yanzu, hamsin a garin Abuja, hamsin a jihar Kano. Amma muna sa ran ƙara motoci cikin wata uku da fara aiki. Kuma App ɗinmu ‘bridge’ ne wanda zai yi haɗa fasinjoji da direbobi. Wajen rajista akwai na fasinjoji da kuma na direbobi.

Neptune Hausa – Me ya jawo ra’ayin ka akan manhajar?

Muktar – Rashin abin yi ga matasa ne ya janyo ra’ayi na, da kuma rashin ilimin kimiyya da fasaha a jihohin arewa. Ina sa ran cire dubban mutane daga cikin wannan matsalar. Wannan manhajar zai samar da aikin yi ga mutum sama da dubu goma cikin wata uku.

KU KUMA KARANTA: Manhajar ‘Threads’ da yadda ake amfani da ita

Neptune Hausa – Yaushe za a fara anfani da manhajar?

Muktar – Za mu fara amfani da shi a garin Abuja a ranar 15 Disamba, 2023.
A jihar Kano kuma ranar 17 Disamba, 2023 da yardar Allah. Daga wannan ranar zaka sami manhajar a Play store, Apple store, IOS.

Muktar Auwal

Neptune Hausa – Kana da masu ɗaukan nauyin wannan manhajar ne?

Muktar – Ni kaɗai ne, bani da wanda ke ɗaukan nauyin. Amma ina so in akwai masu ɗaukan nauyin, ina maraba da su.

Neptune Hausa – Me burin ka?

Muktar – Ina son na faɗaɗa wannan manhajar ta isa duk jihohin arewacin Najeriya. Da kuma buɗe iyakoki a duk jihohin.

Neptune Hausa – Akwai abubuwan da za mu tsammani nan gaba?

Muktar – Ƙwarai kuwa, ina sa ran ƙara motoci wanda zai dinga tafiye-tafiye daga gari zuwa gari. Da kawo bas na ɗaukan mutane dayawa.

Neptune Hausa – Daga ƙarshe me za ka ce?

Muktar – Ina godiya ga Allah da ya bani damar buɗe wannan manhajar, ina kuma kira ga matasa musamman ƴan arewa da kada su karaya a burikan su.

Neptune Hausa – Mungode da bamu lokacin ka.

Muktar – Ni ma nagode.

Continue Reading

Labarai

Shugaban Daylight Reporters ya ziyarci ofishin Neptune Prime a Abuja

Published

on

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin dillancin labarai na jaridar yanar gizo ‘Daylight Reporters’ Ɗahiru Hassan Kera, ya kai ziyarar girmamawa ga ofishin kamfanin Neptune Network Nigeria Limited, mawallafin jaridar Neptune Prime sashen Turanci da Hausa Dakta Hassan Giɓma ne ya tarbe shi a babban ofishinta dake Abuja.

A lokacin ziyarar, Kera da Dakta Hassan Gimba, Mawallafi kuma Shugaban Kamfanin Neptune Network Nigeria Limited wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Mabambantan Arewa-maso-Gabas, sun tattauna yadda za a ba da gudummawar ci gaba da kuma ci gaban yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.

KU KUMA KARANTA: Shugaba kamfanin Neptune prime, Hassan Gimba, ya taya Gwamna Buni murnar sake lashe zaɓe

Kera wanda ya fito daga jihar Gombe kuma shugaban ƙungiyar malaman sadarwa da ƙwararru ta Nijeriya (ACSPN) daga yankin Arewa maso Gabas, ya jaddada muhimmancin magance matsalolin da yankin arewa maso gabas ke fuskanta domin ta haka ne kaɗai zai iya bunƙasa ƙasar nan.

Ya bayyana buƙatar saka hannun jari a ɓangaren ababen more rayuwa, kamar kyawawan hanyoyi, wuraren kiwon lafiya, da cibiyoyin ilimi. Shugabannin biyu da suka fahimci ƙalubalen da yankin ke fuskanta na ganin cewa, haɗin gwiwa kan wani shiri na bunƙasa yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya wani mataki ne mai kyau na magance ƙalubalen da yankin ke fuskanta, da kuma bayar da gudumawa ga ci gaban Nijeriya baki ɗaya.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like