Mun Amince Da Saliu Mustapha Ya Zama Shugaban APC – Kungiyoyin Arewa

0
701

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

GAMAYYAR kungiyoyi masu zaman kansu daga arewacin tarayyar Najeriya masu dangantaka da Jam’iyyar APC sun bayyana goyon bayansu ga Malam Saliu Mustapha da ya zama shugaban Jam’iyyar, musamman ganin irin yadda wannan bawan Allah ke nuna goyon bayansa a fili ga shugaba Muhammadu Buhari, kuma shugaban kasa Buhari ya bayyana karara kwanan nan a fili irin kudirinsa na ganin matasa masu tasowa sun sami dare wa kan madafun iko a cikin Jam’iyyar a babban taron da za a yi na kasa kwanan nan.

A wajen taron da gamayyar kungiyoyin suka yi a ranar satin da ya gabata a Kaduna, kungiyar ta CNNRG sun bayyana Mustapha a matsayin matashin da ke da tsari da akida irin na shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dace a bashi dukkan hadin kai da goyon bayan da ya dace, musamman kasancewar yadda shugaban kasa ya karbi tawagar matasan APC na kasa a fadarsa da ke babban birnin tarayya Abuja.

A cikin takardar bayanin bayan taron da aka yi mai dauke da sa hannun Kwamared Isah Abubakar na kungiyar, majalisar hadin kan matasan Arewa ta kasa da Salihu Dan Lami na kungiyar matasan arewa (AYA), gamayyar kungiyoyin sun bayar da tabbacin cewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar CPC na kasa zai taimaka kwarai a samu ingantaccen ci gaban kasa baki daya.

Gamayyar kungiyoyin suka ce: a matsayinsa na mafi karancin shekaru daga cikin jerin yan takarar, Mustapha zai zama wani mutum da ya zama katanga tsakanin yan takarar da suka tsufa, da kuma matasa masu dabbaka tsarin Dimokuradiyya da suka kasance na da kashi sama da Hamsin (50) na yawan masu kada kuri’a. Don haka wannan zai bayar da wata damar APC ta samun nasarar lashe dukkan zabukan da za a yi nan gaba.

“Kuma shi wannan dan takara namu ba wani abu da ya danganta shi zama bako a koda yaushe da ke ziyarar hukumar yaki da masu almundahanar kudi da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, kamar yadda wadansu da suke neman wannan matsayi na shugabancin APC a matakin kasa baki daya, suka kasance sakamakon zargin da hukumar ke yi masu wanda ya sa dole suke kai ziyara hukumar.

“Wannan ne ya Sanya ya zama jakada nagari ga shugaba Buhari musamman a bangaren batun yaki da cin hanci da rashawa da Gwamnatin Gwamnatin Sanya a gaba, wannan ma ya bambanta shi da wasu yan takarar da suka kasance masu hannu a cikin badakalar kudi da ake zargin Daduki da su na batun sayo makamai.

Kuma Mustapha zai kasance babban jakadan shugaba Muhammadu Buhari da zai kasance ya ci gaba da duba ainihin nasarorin da Gwamnatin Buhari Buhari samu bayan kammala wa’adinsa a shekarar 2023.

Taron gamayyar kungiyoyin da ke kokarin farfadowa rare da kara inganta al’amuran kasa daga arewacin Najeriya, sun ce hakika lamari ne mai matukar amfani a duba al’amarin siyasar Mustapha da kuma tsarin rayuwarsa domin muhimmancinsu ha al’ummar kasa baki daya.

“Kuma shi ne kawai dan takarar da ke da kwarewa ta musamman a APC a dukkan jerin yan takarar da suke neman wannan matsayin”.

“A matsayinsa na wanda ke rike da sarautar gargajiya ta Turakin Ilori, ya kasance mutum mai matukar ganin girman sarautun gargajiya wanda hakan ya Sanya a koda yaushe yake matukar girmamasu, saboda haka bayar da shugabancin jam’iyyar APC ga Saliu Mustapha zai taimaki Najeriya da yan kasar baki daya a kai ga Tudun muntsira.

“Kamar yadda kowa ya Sani shi mutum ne mai taimako da ba za a iya kwatanta irin kokarinsa ba a dan Takaitaccen lokaci domin a kullum shi burinsa shi ne ya taimakawa marasa karfi su fita daga cikin halin talauci da duk wani nau’i na babu, wanda hakan ya sa yake samawa matasa dalibai taimakon karatun makaranta domin su samu cika burinsu a rayuwa”, inji gamayyar kungiyar matasan.

Gamayyar kungiyoyin na arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa sakamakon irin la’akari da nagarta da ingancin da Saliu Mustapha ke da shi ne ya dace a bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Saliu Mustapha, ya dare kujerar shugabancin APC na kasa domin a samu ci gaban da kowa ke bukata.

Leave a Reply