Karamar Hukumar Dawakin Tofa Ta Ciri Tuta Wajen Bunkasa Ilimi

0
713

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

BABU shakka, majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa tana ci gaba da samun kyawawan nasarori a fannin ilimi musamman duba da yadda zababben shugaban karamar hukumar, Alhaji Ado Tambai Kwa yake Kara kokari wajen samar da yanayi mai gamsarwa ta fuskar koyo da kuma koyarwa a fadin karamar hukumar.

Sannan duk da irin kalubalen da ake ciki na tattalin arziki wanda ya shafi duniya baki daya, amma shugaban Ado Tambai bai nuna gajiyawa ba wajen hidimtawa ilimi na addini da kuma na zamani wanda hakan ta sanya karamar hukumar Dawakin Tofa ta Ciri tuta wajen samar da yanayi mai Kyau a fannin ilimi.

Wani abin ban sha’awa ita ce, karamar hukumar tana kuma kokari wajen samarwa dalubai makarantu dake sauran sassa daban-daban na kasarnan domin ganin sun sami ilimi ingantacce wanda kuma zai zamo alheri ga kasa baki daya.

Akwai dalubai masu tarin yawa da ke karatu a makarantu daban-daban wadanda kuma karamar hukuma ce ke daukar dawainiyar kai su makarantun da kuma dawo dasu idan anyi hutu wanda ko shakka babu hakan abin alfahari ne ga al’umar karamar hukumar ta Dawakin Tofa.

Duk da cewa babu lokacin da za’a fayyace dukkanin nasarorin da Alhaji Ado Tambai Kwa ya samu a bangaren ilimi ba, amma dai zan dan bayyana wasu daga cikin abubuwan da tarihi bazai manta da shi ba saboda hidimar da yake yiwa harkar ilimi.

Sannan kuma karamar hukumar Dawakin Tofa tana kokari wajen gudanar da gyare-gyaren makarantu da sabunta su har ma da kewaye wasu daga cikin makarantun ta yadda zasu ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai gamsarwa ta fuskar bada ilimi da tarbiyya.

Duk wanda ya ziyarci yankin karamar hukumar Dawakin Tofa zai hakikance cewa fannin ilimi yana samun kulawa daga shugaban karamar hukumar ta Dawakin Tofa da mataimakan sa kan harkar ilimi wanda hakan ya taimaka wajen bunkasa koto da koyar was a dukkanin makarantun yankin.

Cikin hidimomi da Alhaji Ado Tambai Kwa ya gabatar akwai biyawa yara kudin jarrabawa, da raba kayan karatu a mazabu 11 na karamar hukumar kamar kayan rubutu da kayan sawa watau (Uniform) da kuma litattafai da sauran abubuwa na koyon karatu inda kuma iyayen yara suke ci gaba da yiwa majalisar karamar hukumar addu’oi.

Alhaji Ado Tambai Kwa ya kuma kasance shugaban karamar hukuma mafi kwazo wajen tallafawa ilimi wanda kuma ya kasance a sahun gaba wajen kawo sauyi a fannin zamantakewa.

A nasa bangaren, Ado Tambai Kwa ya bayyana cewa ” muna kokari wajen bunkasa ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa domin ganin ana samun yara masu hazaka wadanda kuma zasu ci gaba da kasancewa jakadu nagari a dukkanin inda suka sami kansu”.

Leave a Reply