APC A Kano: Za A Sami Maslaha Kafin Babban Taro Na Kasa – Mustapha Gwarzo

0
437

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

JAGORAN kungiyar matasan Kano ta Arewa Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya ce za a sami daidaito a rikicin shugabanci da ya dabaibaye Jam’iyyar a Jihar kano duba da yadda bangarori daban-daban suke kokari wajen samar da maslaha a Jam’iyyar.

Kwamared Mustapha, a yi wannan bayani ne a ganawarsa da wakilin mu, inda ya jaddada cewa wannan rikici ba zai kassara nasarorin da Jam’iyyar zata samu ba a zabukan shekara ta 2023, tare da bayyana cewa wannan rigima zata zo karshe cikin yardar Allah musamman yadda kowane bangare yake fatan ganin an daidaita ba tare da jinkiri ba.

Kwamared Mustapha Gwarzo yayi Kira ga dukkanin ‘ya’yan Jam’iyyar ta APC a Jihar kano da su kara nuna goyon bayan su ga batun sulhun da ake kokarin samarwa ta yadda Jam’iyyar zata ci gaba da kasancewa cikin nasara musamman ganin cewa babban taron fitar da shugabanni na matakin kasa yana matsowa.

Jagoran matasan yayi anfani da wannan dama inda ya godewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa namijin kokarin da yake yi wajen aiwatar da managartan aiyuka a fadin Jihar kano, kuma bisa la’akari da bukatun kowane bangare, tare da yin alwashin ci gaba da bada gudummawar sa wajen bunkasa Jam’iyyar ta APC da kuma hada kan matasa.

Leave a Reply