Miyar Kifi (Nsala)

0
358

Daga Fatima MONJA Abuja

Shin wai farfesu kaɗai kuka iya da kifi ko kuna sarrafata shi ta wasu hanyoyin daban? Uwargida ta gwada wannan miyar ‘yar asalin garin Onicha.

Abubuwan buƙata

Kifi tarwaɗa
Attarugu
Albasa
Ganyen shuwaka ko utazi
Tafarnuwa(in kana so)
Doya/Makani/Gwaza

Carafish

Maggi

Yadda zaa hada
Da farko uwargida zata samu ruwan zafi ta zuba kan kifin ta zata ga wannan yaƙin bayan kifin yana fita. Haka za a cigaba da wanke tarwaɗan ya zama fari har zai dinga ɗan tashi saman ruwa, sai a tace a sa hannu ki wanke kifin ki tas sai ya zama ba yauki ko kaɗan sai a ajiye.

Ki dafa doyan ki ko makanin ki dakashi yai laushi sosai sai a ajiye shi gefe sai ki kawo attarugu, albasa, tafarnuwa, crayfish da ganyen shuwaka kaɗan in kina da shi ƙwaya daya in ganyen utazi ne shima ƙwaya daya dan kar yai ɗaci. Sai a jajjaga su waje ɗaya.

Sai uwargida ta samu tukunya ta zuba kifin ta sa sinadarin ɗandano, a zuba ruwa dai-dai kan kifin ta ɗaura kan wuta har sai ya tafasa sai ta ɗauko jajjagen ta zuba, a barshi kaman minti goma sai a zuba wannan dakakkiyar Doya ko Makanin a zuba ba dayawa ba har sai ya narke don miyar ta ɗanyi kauri. Shikenan angama Miyar Nsala za’a iya yowa mai gida da sakwara,Semo,Fufu,Teba hmmm Ba’aba ma yaro mai ƙiwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here