Mazauna Birnin Gwari sun ce ba sa iya barci sai da rana saboda fargabar ‘yan fashin daji

0
225

Daga Wakilinmu

'Yan fashin daji

Mazauna yankin Birnin Gwari da ke jhar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da kasancewa cikin fargaba, sakamakon ƙaruwar satar mutane, da hare-haren ƴan fashin daji a yankin.

Ko da a baya-bayan nan sai da aka yi garkuwa da mutane 17 a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari bayan barayin sun tare motocin da suke ciki.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Hausa cewa duk da yake akwai jami’an tsaro a hanyar, masu garkuwa da mutane suna cin karensu babu babbaka a yankin.

Ya ce,” A ranar Juma’a masu garkuwar sun tare wasu motocin fasinja da ke kan hanyar zuwa Buruku, inda suka ɗauki mutum bakwai wadanda ‘yan kasuwa ne da suka je cin kasuwa.

”A washegarin da aka sace mutanen ma wasu ‘yan fashin dajin sun sake tare hanya inda suka dauki mutum goma, daga bisani daya daga cikinsu ya gudo inji mazaunin yankin.

Mutumin ya ce dama jama’ar yankin nasu ba sa bacci yana mai cewa “idan dai mutum na son ya yi bacci to sai dai ya yi da rana, saboda kullum a cikin zulumin abin da zai iya faruwa muke.”

“Ba a yin kwana uku a jere ba a sace mutane a hanyar Birnin Gwari ba, wannan abu yana damunmu matuka, muna so gwamnati ta kara jami’an tsaro a wannan hanyar,” in ji mazaunin yankin.

Jihar Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da suke fama da matsalar tsaro a Najeriya kuma musamman a yankin arewaci.

Kazalika Birnin Gwari na daya daga cikin wuraren da wannan tsaro ya fi tabarbarewa a cikinsu, wanda da wuya a yi mako guda ba a kai hari ko an sace wani ba a yankin.

Wasu dai na ganin ma’adinan zinaren da ke karkashin kasa a yankin na cikin abubuwan da suka sa aka tsananta kai hare-hare a yankin nasu.

A baya baya nan rahotanni sun ce rundunar sojin saman Najeriyar ta yi nasarar tarwatsa wani gungun ‘ya fashin daji da ke addabar matafiya a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda aka kashe fiye da mutum 45, ciki har da jagoransu mai suna Ali Kwaja.

Leave a Reply