Yadda Sashen Sadarwa Na Kamfanin KEDCO Ke Inganta Hulda Da Al’uma

0
249


JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
Babu shakka, sashen Sadarwa na kamfanin samar da hasken wutar lantarki watau (KEDCO) yana cimma gagarumar nasara waken bunkasa  hulda da al’uma tareda kyautata dangantataka tun lokacin da shugaban sashen kula da sadarwa malam Ibrahim Sani Shawai ya karbi ragamar wannan sashe.
Na lura da cewa sashen kula da Sadarwa da kuma hulda da al’uma na kamfanin KEDCO yana kokari sosai wajen tabbatar da cewa akwai dangntaka mai kyau tsakanin sa da mutane dake iya hurumin ikon kamfanin watau jihohin kano da Jigawa da kuma katsina.
Haka kuma babban abin lura shine yadda Sashen sadarwa da hulda da Al’uma na kamfanin KEDCO ya ciri tuta wajen isar da sakonni daga kamfanin zuwa ga al’umomin dake jihohi uku da ke karkashin sa, wanda hakan yana taimakawa wajen samar da yanayi maikyau na tafiyar da hulda bisa tsarin samar da hasken wutar lantarki mai inganci.
Bisa irin namijin kokari na  sashen sadarwa da hulda da jama’a na kamfanin KEDCO, dukkanin tsare-tsare da shirye-shiryen kamfanin suna isa ga abokan hulda, sannan ana ci gaba da samun fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu duba da yadda yanzu haka ana samun wutar lantarki sosai kuma a birane da yankunan karkara na jihohin da kamfanin  ke baiwa wuta.
Yana dakyau al’uma  kuma abokan huldar kamfanin KEDCO su sani cewa sashen sadarwa da hulda da jama’a yana kokarin tabbatar da isar da dukkanin wani sako daga hukumar kamfanin don haka a ci gaba da aiki da dukkanin sakonnin dake fitowa daga sashen bisa shugabancin malam Ibrahim Sani Shawai.


Leave a Reply