Mayaƙan ISWAP Sun Sace Yara Mata Da Maza 20 A Jihar Borno

0
437

MASU iƙirarin jihadi da ake zargin ‘yan ƙungiyar ISWAP ne sun kashe mutum biyu tare da sace wasu yara 20 a kusa da garin Chibok na Jihar Borno ranar Alhamis.

Wani shugaban yankin ya faɗa wa manema labarai cewa maharan sun afka wa garin Piyemi, inda suka yi awon gaba da mata 13 da maza bakwai.

A cewar mazauna yankin, mayaƙan na Islamic State West Africa Province (ISWAP) sun afka wa garin ne da rana cikin kakin sojoji suna harbe-harbe tare da sace kayayyakin shaguna, sannan suka dinga ƙona gidaje.

“Sun harbe mutum biyu sannan suka sace yara mata 13 da maza bakwai, shekarunsu 12 zuwa 15,” kamar yadda mazaunin yankin Samson Bulus ya faɗa wa AFP.

Wani mai suna Silas John ya ce “maharan sun zuba yaran 20 cikin wata motar a-kori-kura da suka ƙwace a ƙauyen kuma suka shiga daji da su”.Article share t

Leave a Reply