Atiku Ya Ce Wajibi Ne A Hukunta Wanda Ya Kashe Hanifa

0
246

“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa gane yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta tare da kashe ta.” Atiku ya ce cikin sanarwar da ya fitar.WASHINGTON — 

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya nuna alhininsa bisa kisan da masu garkuwa da mutane suka yi wa Hanifa ‘yar shekara 5 a Jihar Kanon Najeriya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Atiku Abubakar, ya kwatanta lamarin a matsayin “mummunan labari.”

“Na samu mummunan labarin kisan gilla ga yarinya Hanifa ƴar shekaru 5, wadda aka kashe bayan kwashe kwanaki 47 a hannun masu garkuwa.

“Wannan dabbanci da rashin imani ne. Na kasa gane yadda mutum mai hankali zai raba yarinya karama da iyayenta tare da kashe ta.” Atiku Abubakar, ya ce cikin sanarwar da ya wallafa.

Leave a Reply