Kungiyar NCWS  Reshen Jihar Kano Ta Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hanifa

0
248


JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

Kungiyar matan Nijeriya  ” National Council For Women Societies ” (NCWS) ta aike saw sakon ta’aziyya ga gwamnatin jihar kano da iyayen yarinyar da aka sace kuma aka kashe watau Hanifa Abubakar tareda fatan Allah ya gafarta mata ya kuma baiwa iyayen ta hakurin jute wannan rashi.
A cikin watau sanarwa da shugabar kungiyar ta bayar, Hajiya Zainab Ali Musa ta nuna alhinin kungiyar ta NCWS danger da wannan babban rashi da akayi, tareda yin Kira ga mahukumta da su yi hukunci mai rsanani kan dukkanin wadanda aka sacewa da hannu a sacewa da kuma kashe Hanifa Abubakar.
Haka kuma kungiyar tayi addu’ar Allah ya gafartawa wannan yarinya tareda jaddada cewa lallai anyi babban rashi da kuma fatan dukkanin  masu hannu a wannan danyen aiki zasu fuskanci hukunci daidai abin da suka aikata, sannan kungiyar tayi Kira ga iyaye da su ci gaba da kulawa da yaran su da kuma yin addu’oi na neman tsari.

Leave a Reply