Matan Arewa Don Tinubu Sun Bukaci Masu Ruwa Da Tsaki Na APC Su Marawa Burin Bola Tinubu Baya

0
380

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GABANIN zaben fidda gwanin Jam’iyyar (APC) mai zuwa, kungiyar Matan Arewa domin Tinubu wato (Arewa Women for Tinubu), ta yi kira da masu ruwa da tsaki a kasar nan da su marawa burin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya a yunkurinsa na kawo sauyi a kasar nan don samun kyakkyawar makoma.

Shugabar kungiyar Hajiya Sa’adatu Garba Dogon Bauchi ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da manema labarai a ranar Laraba yayin wani taro da aka gudanar a garin Kaduna, inda ta bayyana cewa, Tinubu ya kasance dan takarar shugaban kasa daya tilo da ke da kasar a zuciyarsa.

Sa’adatu ta kuma bayyana Tinubu a matsayin mutum mai gaskiya, mai gina al’umma, inda ta ce yana da sha’awar tallafa wa sana’o’in mata da kuma son cika burinsu na siyasa.

Ta kara da cewa, makasudin gudanar da taron shi ne domin neman goyon baya ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu daga mahalarta taron kan burinsa na zama shugaban kasar Najeriya a shekarar 2023.

Hajiya Sa’adatu ta kuma roki wakilan Jam’iyyu na kasar da su fara yin la’akari da yanayin muradin kasar ta hanyar zaben mutane masu gaskiya da za su iya kawo ci gaba mai kyau a lokacin zaben fidda gwani na Jam’iyyar.

Bugu da kari, ta shawarce su da kada su fifita samun kudi a kan hakkokin da ake bukata game da ‘yan takarar da ke da tarihin da ake iya gani.

Ta ce, “game da batun masu zaben yan takara, zan iya ba da shawarar cewa kada su nemi kudi, su zabi wadanda suka dace, domin kudin nan za su kare, don haka su duba rayuwar ‘ya’yanmu da jikokinmu.”

Ta ci gaba da cewa, nasarar da dan takarar shugaban kasar ya samu a karkashin jam’iyyar APC na da yawa musamman kan yadda ya canza tare da bunkasa Jihar Legas a lokacin da yake gwamna.

A nasa jawabin, Sanata Sani Saleh ya ce taron an yi shi ne domin sanar da mahalarta taron bukatar yin kira ga wakilan jam’iyyar APC da su zabi Tinubu.

Ya kara da cewa, daga cikin duka yan takarar Shugabancin Kasar, babu wani dan takarar da yafi cancanta a yanzu da zai iya warware matsalolin da ake fuskanta a kasar fiye da Bola Tinubu wanda ya yi a shekarun baya dukda suna yar-tsama da Shugaban Kasar lokacin, kuma kowa ya shaida Jajirtacce sannan haziki a fannin shugabanci.

Taron ya tattaro mata daga jihohin arewa daban-daban da sauran masu ruwa da tsaki da nufin cimma burin buri.

Leave a Reply