Ku Yi Amfani Da Kuri’un Ku Wajen Tumbuke Gwamnati – Shehu Sani

0
418

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

TSOHON Sanatan yankin Kaduna ta tsakiya, kwamared Shehu Sani ya yi kira ga daukacin Talakawa da su tabbatar da sun yi amfani da kuri’unsu wajen kokarin canza duk wata Gwamnatin da ba sa ra’ayin ta har sai sun tumbuke ta baki daya.

Sanata Shehu Sani ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a wajen babban taron da ya yi da su a cibiyar kungiyar Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna.

Kwamared Shehu Sani, ya kuma yi kira ga daukacin ‘yayan Jam’iyyar PDP da su hada kansu ta yadda za a samu damar cimma bukatar nasarar lashe zaben da ke tafe a shekarar 2023.

Kwamared Sani ya kuma yi kira ga masu zaben yan takarar da suke wakilan Jam’iyyar da su tsayarwa Jam’iyyar dan takarar Gwamna nagari, kana su guji siyasar kudi domin ba ta da wani amfani a gare su da iyalansu da dukkan yan uwa baki daya.

Ya ce, “ta yaya kai deliget wanda aka zaba ba tare da kudi ba sai ka ce sai wani ko wasu sun baka kudi, bayan ka san hakan illa ce babba a wajen ka da sauran yan uwa, don haka ina kira ga wakilan Jam’iyyar da su tabbata sun zabi na kirki daga cikin yan takarar Gwamnan da ake da su a karkashin Jam’iyyar ta PDP a Jihar Kaduna”.

Ya kuma tabbatarwa da manema labarai cewa idan masu zaben dan takara suka zabe shi ya zama Gwamna, ba shakka za a ga abin mamaki kwarai, domin akwai ingantaccen tsari sosai mai inganci da zai kai PDP ga samun nasarar da za ta amfani kowa.

Sai dai Sanata Shehu Sani ya ce shi ba yaron wani ko wasu ba ne a harkar siyasa don haka lamarin ya kasance a lokacin da ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar da ya bari kuma duk da haka ya samu nasara cikin hukuncin ubangiji.

Ya kuma tabbatarwa da manema labarai cewa nasara na tare da jam’iyyar PDP da kuma yayanta domin a samu nasara.

Kwamared Shehu Sani ya kuma bayar da tabbacin tafiya da duk wani dan Jihar Kaduna tun daga bayar da Kwangiloli, da sauran ayyukan tafiyar da Gwamnati. Kuma ya yi kira ga mutanen yankunan karkara da su himmatu wajen bashi dukkan goyon bayan da ya dace saboda Gwamnatin da zai kafa ta su ce ta sanin mutunci da martabar jama’a a ko’ina suka fito.

“Ba kamar yadda lamarin yake ba a halin yanzu da akasarin mutanen yankunan karkara ba su san ma abin da ake ciki ba game da aikin da ake a Jihar duk da akwai kudinsu a hannun Gwamnati”, inji shehu Sani.

“Zan tabbatar da na gudanar da aiki tukuru wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a Jihar Kaduna”.

Leave a Reply