Makarantar haddar Alkura’ani ta Ahbab ta garin Kwaftara ta yaye Dalibai  93

0
439

Daga Isah Ahmed, Jos
Makarantar koyar da haddar Alkura’ani mai girma, ta Madinatul Ahbab ta garin Kwaftara a kusa  garin Saminaka da ke Jihar Kaduna, ta gudanar da bikin yaye dalibanta karo na 31, inda ta yaye dalibai guda 93, a ranar asabar din da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen taron yaye daliban,  Shugaban Makarantun Madinatul Ahbab na Kasa Khalifa Sayyadi Ahmad Dan-Almajiri, ya bayyana cewa wannan yaye dalibai, wani babban abin farin ciki ne ga al’ummar musulmin  duniya gabaki daya.
 Ya ce babban abin da suka sanya a gaba shi ne ilmintar da ‘yayan al’ummar musulmi, domin su fahimci ilmin addini musulunci da na zamani.

”Don haka ya zuwa yanzu muna da  makarantu sama da 260 a sassa daban daban  na kasar nan, da Kasashen Nijar da Kamaru da Mali. Daga cikin daliban da    muka yaye  akwai  wadanda suka zama Alkalai da malaman jami’o’i da likitoci da dai sauransu”.
 Ya yi kira ga gwamnatoci da sauran masu hali, su rika taimakawa irin wadannan  makarantu na hadda Alkura’ani mai girma. Saboda kokarin da   suke yi, na  fitar da matasa masu taimakawa kasa da cigabanta.
 Ya ce daliban irin wadannan makarantu, basa shaye-shaye da sace sace da ta’addanci. Don haka  ya zama wajibi ga gwamnati ta rika taimakawa irin wadannan makarantu.
Da yake jawabi wajen, Shugaban masu wa’azi na Makarantun Madinatul Ahbab na Jihar Kaduna, Sheikh Nazifi Ibrahim Zariya ya bayyana cewa, a duk duniya babu falalar da Allah ya yiwa dan’adam,  kamar Alkura’ani. Don haka  ya yi kira ga al’ummar musulmi, su godewa Allah kan wannan ni’ima da  ya saukar mana, kuma su rike wannan Alkura’ani suyi aiki da shi.
Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban Makarantar ta hadda Alqura’ani ta Madibatul Ahbab ta garin na Kwaftara, Alhaji Adamu Halilu Kwaftara ya bayyana cewa, a wannan ya ye dalibai da suka yi na bana karo na 31, sun yaye dalibai da suka sauke Alkura’ani mai girma guda 79, a yayinda suka yaye dalibai guda 14 da suka hadda ce Alkura’ani mai girma.
‘’Daga lokacin da muka bude wannan makaranta zuwa yanzu, mun yaye dalibai sama  3000. A cikin daliban wannan makaranta akwai wadanda suka tafi jami’o’i a nan gida Najeriya har kasar Indiya. Wasu   sun gama jami’a suna karantarwa, wasu  sun sami ayyukan gwamnati a wurare daban daban. Muna samun dalibai daga sassan jihohin Filato da Nasarawa da Kano da Bauchi da Katsina’’.

Leave a Reply