Kungiyar marubuta ta Arewa reshen Filato  ta gudanar da taron shekara

0
377


Daga Isah Ahmed, Jos
Kungiyar Marubuta ta Arewa a kafofin sada zumunta, [Arewa Media Writers] reshen Jihar Filato, ta gudanar da babban taronta na shekara, a karshen makon da ya gabata, a dakin taro na Abba na Shehu unity  da ke  garin Jos.
  Shi dai wannan taro na bana,  an shirya   shi ne  domin karfafa hadin kai tsakanin kungiyoyin matasa da ke cikin garin Jos, da ayyukan su suka shafi amfani da zaurukan sada zumunta, domin faxakarwa kan abubuwan da suka shafi, kafofin sada zumunta.
 A wajen  taron,  masana   kan fannin sadarwa, watsa labarai, koyar da ilimin fasahar zamani ta ICT, fitattun marubuta a shafukan sada zumunta  sun  ja hankalin mahalarta taron, game da muhimmancin tsaftace yadda suke rubuce rubuce, a zaurukan sada zumunta, musamman na Facebook, WhatsApp da sauran su. 
 Da yake jawabi a wajen taron, wani Shugaban al’umma kuma Makaman Jos, Injiniya Mansur Salihu Nakande ya yi kira  ga  matasan Arewa, su hada kai wajen amfani da murya daya, a cikin rubuce rubucen su, ta yadda za a samar da shugabanci nagari da  zaman lafiya da  tsaro da bunkasa harkokin ilimi, musamman ilimin ICT.
 Itama a nata jawabin, Hajiya Kaltume Auwal, da ke Sashin koyar da ilimin fasahar ICT a Jami’ar Jos, ta yi bayani game da rabe raben manhajojin sada zumunta da yadda suke amfanar da al’umma, da kuma hadarin su ga jama’a.
Shima a nasa jawabin, wani masanin fasahar sadarwa ta ICT, Mr Kabir Ishak ya koyar da mahalarta taron,  rabe raben manhajonin kafafen sadarwa da kalubalen da ake fuskanta, ta hanyar amfani da zaurukan sada zumunta, da  yadda mutum zai magance matsalolin da shafukan sa na Facebook, Instagram da sauran su ke fuskanta. 
 Tun da farko a nasa jawabin, Shugaban kungiyar reshen Jihar Filato, Malam Abba Abubakar Yakubu, ya ce   koiarin cike gibin da ke tsakanin mabanbanta addini da al’ada a jihohin oasar nan, na aaya daga cikin manufofin kungiyar.
 Ya ce kungiyar  na kokarin samar da zaman lafiya da fahimtar juna ta hanyar amfani da hikimomi  a rubuce-rubucen ta.
Daga nan ya shawarci matasa da kada, su  rika yarda  ana amfani da su wajen kawo matsaloli a cikin al’umma, 

Leave a Reply