Kungiyar Matan Fulani Sun Buƙaci Jami’an Gwamnati Da Su Daina Cin Zarafin Su

0
575

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA kungiyar matan fulani ta, Rube Fulbe Global Rights and Development Initiative, ta bayyana damuwarta kan yadda jami’an tsaro ke tafiyar da al’amura musamman ganin yadda aka yiwa wasu makiyaya fulani a wani faifan bidiyo na baya-bayan nan.

Da take zantawa da manema labarai a garin Kaduna, Shugabar kungiyar, Hajiya Halima Usman, ta ce dole ne su bayyana damuwarsu bisa la’akari da irin yanayin muguntar da aka yi wa mazajensu.

Ta ce “Mun zo nan ne domin nuna damuwarmu kan lamarin da ya faru makonni biyu da suka gabata a yankin Kakura da ke karamar hukuma chikun ta Jihar Kaduna inda aka yi kuskuren cewa wasu Fulani ‘yan fashi ne alhali ba su ba ne.”

Halima ta ci gaba da cewa, ba su ji dadin yadda jami’an tsaro ke jefa wadannan mutane cikin motar ba, suna daukar su tamkar dabbobi.

“Muna nan muna yi wa gwamnati kuka a matakin Tarayya da Jihar da ta yi taka-tsan-tsan da wannan lamarin, duba da irin muguntar da aka yi masu a lokacin da ake kiransu da ‘yan fashi.

Wannan dai ba shi ne karon farko da irin wannan lamarin ke faruwa ba, an dade ana tafkawa wanda a mafi yawan lokuta zaka ga ’yan banga suna far wa mazajenmu suna sace musu shanu, idan kuma suka rama ko yi kokarin karbo shanunsu, sai a bayyana su a matsayin ‘yan fashi. Ta ce

Ta yabawa gwamnatin Jihar Kaduna bisa matakin gaggawar da ta dauka duk da cewa mutanen nasu sun samu raunuka yayin da aka sako gawarwakin mutanen uku da aka kashe yayin harin kuma an yi musu jana’iza.

“Duk da haka, muna son gwamnati ta taimaka wa wadannan mutane ta hanyar biyan su diyya da aka yi musu ko kadan hakan zai rage musu radadin wahala.”

“Ta bayyana cewa, kalubalen da Fulani Makiyaya ke fuskanta a kasar nan shi ne yadda wasu jami’an tsaro ke kai wa al’ummarsu farmaki suna kwashe dabbobinsu, idan aka yi kokarin dawo da su, sai a bayyana su a matsayin ‘yan fashi.

“Wannan ba daidai ba ne, rayuwa fulani ba ta cikin aminci domin duk lokacin da wani abu ya faru za a rika zargin Fulani da aikatawa, rayuwarmu tana cikin hatsari don a mayar da fulani a rayuwar fulani kodayaushe ba a bakin komai ba, shi ya sa muke mika kokenmu, domin a karshe matan ke shan wuya ta yadda za a bar su ba abin da za su ciyar da iyalinsu.”

Daga nan sai Hajiya Halima ta bukaci gwamnati da ta kawo musu dauki musamman a kan matsalar satar shanu da ta ce a gaggauta magance ta.

Idan dai za a iya tunawa, sojoji da ‘yan sanda sun yi karin haske kan cewa mutanen da aka kama a wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta a kwanakin baya, makiyaya ne da aka yi kuskuren cewa wasu ‘yan bindiga ne da suka kai hari a kauyen Kakura da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Taron ya samu halartar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, shugaban karamar hukumar Chikun, Engr. Salasi Musa, mamba mai wakiltar mazabar Chikun a majalisar dokokin jihar, Hon. Ayuba Chawaza, Hakimin Kujama, Stephen Ibrahim, da kwamandan rundunar soji ta 312, Laftanar Kanal D.O Igwilo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here