Aisha Buhari Ta Gayyaci ‘Yan Takarar Shugaban kasa Shan Ruwa Da Sharadin Banda Zuwa Da Waya

0
329

Daga; Rabo Haladu.

MAI dakin Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta shiryawa ‘yan takarar Shugaban Kasa daga jam’iyyu daban-daban liyafa da shan ruwa a fadar shugaban kasa a ranar Asabar mai zuwa, 23 ga watan Afrilun 2022.

Misis Buhari, ta aike da katin gayyata ga ‘yan takarar inda shan ruwan zai gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa da misalin karfe 6:30 na yamma

Katin gayyatar na dauke da sharadin, ‘yan takarar ka da su zo da wayoyinsu yayin amsa gayyatar bude-bakin a fadar shugaban kasa kuma kati da aka aike musu shi ne tikitin shiga wurin da za ayi shan ruwan.

Koda yake umarnin hana shiga da wayar bai shafi mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da gwamnoni da ministocin da za su halarci liyafar ba.

Da ya ke tabbatar da gayyatar, hadimin matar Shugaban kasan a fannin yada labarai, Aliyu Abdullah, ya ce bisa tsari ne da aka saba idan za a yi irin wannan gayyatar ba a barin kowa ya shiga da waya.

Leave a Reply