Rundunar Tabbatar Da Tsaro A Filato Ta Mikawa Cibiyar Takaita Yaduwar Makamai Bindigo 517

0
302

Daga; Isah Ahmed, Jos.

RUNDUNAR tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Jihar Filato (OPSH), ta mikawa Cibiyar takaita yaduwar makamai ta Kasa, bindigogi 517 da ta kwato, a garin Jos. Kwamandan rundunar Manjo Janar Ibrahim Ali ne, ya mika bindigogin.

Da yake jawabi a lokacin da yake mika bindigogin, Manjo Janar Ibrahim Ali ya bayyana cewa, rundunarsa ta OPSH ta kwato wadannan bindigogi ne daga wajen ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuffuka.

Ya ce wadannan bindigogin, sun hada da kirar waje guda 40 da kira gida guda 477.

Kwamandan ya nuna farin cikinsa ga al’umma kan irin rahotannin da suke kawo masu, wanda ya kai su ga wannan nasara da suka samu.

Da yake jawabi a lokacin da yake karbar wadannan makamai, Shugaban Cibiyar takaita yaduwar makamai na shiyar Arewa ta tsakiya, Manjo Janar Hamza Bature Mai ritaya, ya nuna farin cikinsa kan wannan kokari da wannan runduna tayi.

Ya yi kira ga jama’a kan su taimaka, da bayanan da zasu kai ga gano haramtattun makaman da suke hanun jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here