NLC Kaduna Ta Fara Ayyukan Ranar Bikin Ma’aikata Tare Da Yin Addu’o’in Godiya A Coci

0
326

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GABANIN bikin ranar ma’aikata da ake yi a ranar 1 ga Mayu na kowace shekara, kungiyar kwadago ta kasa (NLC), reshen Jihar Kaduna, ta fara gudanar da yin addu’o’in hidimar ayyukan godiya a coci ranar Lahadi 24 ga Afrilu, 2022 a Cocin St. Augustine’s Catholic, dake Kaduna.

Da take jagorantar tawagar NLC ta Jihar zuwa yin hidimar godiyar, Sakatariyar kungiyar, Kwamared Christiana John Bawa, ta ce taron godiya ne na musamman, wanda aka shirya domin fara ayyuka da wayar da kan jama’a gabanin ranar Mayu da za a yi ranar Lahadi mai zuwa.

“Yau muna nan don yin addu’o’in Godiya kafin bikin ranar ma’aikata ta 1 ga Mayu na 2022.

“Muna son yin bukin na bana ne ta hanyar da ta dace, don haka za mu fara da addu’a ga ma’aikata a Kaduna da Najeriya.

“Muna addu’ar Allah ya kawo mana karshen rashin tsaro, mu kuma yi addu’ar ganin an mika mulki cikin lumana a babban zaben shekara mai zuwa.

“Idan babu zaman lafiya, ba za a samu ci gaba ba,” in ji ta.

A cewar ta, sun je coci ne domin wayar da kan jama’a kafin gudanar da ayyukan ranar Mayu.

“A ranar Laraba za mu gudanar da taron karawa juna sani, ranar Alhamis muna fatan za a kai ga samun kulawar likitoci, ranar Juma’a za mu yi Sallah a masallacin SMC.

“A ranar Lahadi za a gudanar da bukukuwan ranar Mayu a filin wasa na Ahmadu Bello, kamar bikin Kirsimeti da Sallah, domin girmama jaruman mu da suka mutu, wadanda suka yi fafutukar ganin mun samu ranar aiki a ranar 1 ga Mayu.

“A jihar Kaduna muna kira ga gwamnatin da ta fara aiwatar da mafi karancin albashin ma’aikata, da ta kuma tabbatar da cewa an mayar wasu daga cikin mambobinmu da aka cire daga tsarin biyan albashi.

“A kowane wata, muna samun korafi daga mambobin kungiyar cewa an cire su daga biyan albashi.

“Muna so gwamnati ta sanya duk wani abu don tabbatar da tsaron ma’aikata, wasu suna aiki a yankunan karkara kuma an yi garkuwa da su.

“Muna kira ga gwamnati da ta tabbatar da tsaro a asibitoci da makarantu a yankunan karkara, muna son gwamnati ta hada hannu da al’umma domin tabbatar da tsaro ga dukkan asibitoci da makarantu a yankunan karkara.

“Muna kira ga gwamnati da ta gudanar da sahihin zabe a shekarar 2023, domin a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

“A wannan karon, ba muna neman karin albashi ba ne, sai dai a biya wadanda ke kan tsarin albashi idan ya cancanta,” in ji ta.

Leave a Reply