MMPAN, Ta Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Hadin Kai Da Zaman Lafiya A Kaduna

0
312

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA kungiyar Kafafen Wallafa Labarai ta Najeriya wato Muslim Media Publishers Association of Nigeria (MMPAN), ta gudanar da taron lakcan karawa juna sani kan hadin kai, zaman lafiya da dauwamar Siyasa a Najeriya gabannin Zaben shekarar 2023 mai karatowa.

A bana, taron mai taken “Matsayin ‘Yan Siyasa, Shugabannin Al’umma Da Kafofin Watsa Labarai” wanda yake shi ne karo na goma kamar yadda aka saba shiryawa a duk shekara musamman a watan Ramadana, ya gudana ne a dakin taro na gidan Sardauna dake Jihar Kaduna a ranar Juma’ar data gabata.

Da yake jawabi a wajen taron, Fasto Yohanna Buru wanda yake Babban mai kula da Cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry, dake Sabon Tasha, kaduna, ya bayyana cewa duk hanyar da za a bi wajen ganin an yada hanyoyin samar da zaman lafiya, wani abu ne da hakan zai taimaka wajen ganin al’umma sun samu natsuwa da kwanciyar hankali.

Fasto Buru, ya kara da cewa wannan taron da Kungiyar ta shirya na daya daga cikin irin abubuwan da suke da’awa a kai ba dare ba rana domin tabbatar an samu dawamammen zaman lafiya a duk wani mataki na rayuwa, wanda hakan yasa ba ya yin kasa a gwiwa wajen ganin ya halarci duk wasu taruruka irin wannan, kuma wanda hakan ya sanya na zama mutum na farko da ya fara amsar lambar yabo daga gare ta.

Ya ce “Allah Ya albarkace mu da yan Jaridu masu hazaka musamman a nan Kaduna, wadanda da jajircewarsu za a iya samun duk wata kyakkyawar alaka tsakanin al’umma, saboda da kuskure kadan idan yan Jaridu za su yi, za a iya samun matsala a cikin al’umma don haka yan Jaridu na rawar da zasu taka domin da su ake shi lunguna da sako yayin yada duk wata da’awa.”

Acewarsa, wajibi ne al’umma su rungumi hanyoyin wanzar da zaman lafiya ta hanyar marawa Gwamnati baya domin ta hakan ne za a iya samun nasara da ci gaban da ake bukata, kana ya shawarci al’umma da yin addu’o’in samun waraka ga kasar daga matsalolin da ta ke fuskanta na rashin tsaro da su gujewa yin abubuwan da za su iya kawo hatsaniya domin akwai ranar hisabi.

Hakazalika a nashi jawabin, Shugaban Kungiyar ma’aikatan mai ta NUPEND, Shiyyar Arewa, reshen Jihar Kaduna, Kwamared Bala Yusuf Ayuba, ya bayyana cewa da hadin kai ne kadai za a iya kaiwa ga duk wata nasarar da ake bukata wanda hakan yasa akoyaushe suke kokarin sun tabbatar da daidaito a tsakanin al’umma musamman ma’aikatansu ba tare da nuna banbancin kabilanci ba.

Ya ce “a namu bangaren, babu ruwan mu da wannan inyamuri ne ko bahaushe ko bayerabe, idan mun tashi yin aiki bama duba kowaye mutum illa kawai aikin muke dubawa, saboda haka ku ma yan Jaridu ya kamata ku tashi tsaye wajen ganin cewa an aiwatar da al’amura daidai domin wannan aiki ba na malamai kadai bane, muma dole mu tashi mu gyara.”

Da yake tsokaci kan manufar kungiyar, Jafar Maitama Yakubu, ya bayyana cewa ita wannan kungiyar an kafa ta ne bisa kudirin ganin an tabbatar da samun zaman lafiya a tsakanin al’umma wanda hakan yasa a duk shekara suke gudanar da wani taron lakca na karawa juna sani a watan Ramadana, kana da karrama wasu al’umma wadanda suka bada gudunmuwa ta fannin samar da jituwa na zaman lafiya a cikin al’umma.

Shugaban Kungiyar, ya kara da cewa, babbar manufarsu a kungiyar ita ce na ganin ta wayar da kan al’umma akowani mataki wanda ya shafi samar da zaman lafiya kuma hakan ke sanya su tattaro al’umma daban-daban da suka hada da yan siyasa, yan Kasuwa, Shugabannin Addini da al’umma masu zaman kansu domin ganin cewa an samu maslaha a tsakanin al’umma.

A karshe, Shugaban Kungiyar MMPAN, Jafar Maitama, ya shawarci al’umma da su rungumi matakin zama lafiya ba tare da nuna banbancin akida ko kabilanci ba wanda da hakan ne kadai za a iya samun ci gaba a kasar baki daya.

Leave a Reply