Kungiyar Makafi Ta Yi Zaben Sabbin Shugabannin Jihar Kaduna

0
300

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

MUTANE masu lalura da nakasar ido karkashin Jagorancin kungiyar makafi ta kasa (NABP), reshen Jihar Kaduna, sun yi Zaben sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin kungiyar na tsawon wasu shekaru hudu nan gaba.

Zaben wanda ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata a cibiyar hukumar kula da masu bukata na musamman ta Jihar Kaduna, an gudanar da shi ne cikin nasara, yayin da wakilai daban-daban na Kungiyar daga kananan hukumomi ashirin da uku na jihar suka hallara domin kada kuri’unsu dangane da zabin son ransu.

A lokacin da yake bayyana wadanda suka lashe zaben, Baturen zaben Malam Musa Sambo Duguza, ya bayyana Mista Jerry Mathew a matsayin zababben sabon shugaban kungiyar bayan ya doke abokin takardar wanda yake shugaban mai ci Malam Haruna Abubakar, sannan kuma Malam Ibrahim Abubakar ya zama sabon mataimakin Shugaban.

Bugu da kari, Sakataren Kungiyar mai ci Mista Isaac Joseph da mataimakin Sakataren, Malam Ahmad Shafi’u duk sun sake darewa kan Kujerarsu yayin da basu da abokan takara, hakazalika sabbin shugabannin duka shiyyoyi uku da aka zaba sun samu nasarar cin Zaben su babu hamayya, sai Umar Muhammad Sani ya zama sabon Jami’in hulda da Jama’a (PRO), Aisha Musa a matsayin Ma’aji, Amina Usman a matsayin shugabar mata, kana sai Yusuf Sha’aibu a matsayin sabon zababben shugaban matasa.

Malam Sambo, wanda yake malami ne kuma shugaban Sashen nakasassu na musamman a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) Zariya, ya nuna jin dadinsa bisa yadda aka gudanar da zaben lafiya, duk da ‘yan kananan kalubale da kura-kurai da aka samu a lokacin zaben, sannan ya buƙaci sabon zababben shugabannin da yin Kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu da yin aiki da tsoron Allah.

A nasa jawabin, babban sakataren cibiyar hukumar kula da masu bukata na musamman nakasassu ta Jihar, Malam Aliyu Haruna Yakasai, ya bayyana yadda aka gudanar da zaben da kuma yanayin yadda ta kasance cikin nasara, adalci da lumana, a matsayin wani babban abun alfari, kana ya bukaci mambobin kungiyar da su rika Kokarin ganin an aiwatar da duk wasu zabukan cikin irin wannan sigar na gaba.

A cewarsa, zaben na masu nakasar ido ya kasance zabe na biyu da ya ke aikin sa-ido wanda ya burge shi ganin irin yadda aka gudanar da shi, domin an gudanar da shi cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin hankali ba, har ila-yau ya yaba wa ’ya’yan kungiyar bisa irin yadda suka gudanar da sahihin zabe duk da cewar mafi yawan wakilan sun fito ne daga kananan hukumomi daban-daban ta Jihar.

Da yake yaba aikin zaben, kodinetan shiyyar Arewa maso Gabas, Malam Halliru Usman, ya buƙaci sabbin zababbun shugabannin Kungiyar da su kasance jakadu nagari ga masu nakasar idon ta hanyar zama wakilai nagari da yin aikin jama’ar suka zabe su akai, sannan da Kokarin samar da karin damammaki ga makafi a Jihar.

Hakazalika, Yohana Ishaku Dangana daya daga cikin wadanda aka zaba a matsayin kodineta na shiyyar ta 3 a Jihar, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda aka gudanar da zaben cikin nasara, sannan ya yabawa mambobin kungiyar ta (NABP) bisa yadda suka gudanar da zaben lami lafiya, yayin da ya roke su da marawa sabbin zababbun shugabannin kungiyar goyon baya na ganin cewa an samu ci gaba da salon shugabancin da ta dace.

Leave a Reply