NUJ Kaduna, Ta Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Horar Da Mambobin Kungiyar

1
291

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR ‘Yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Gidauniyar Bunkasa Kafafen Yada Labarai ta Afrika (AMDF) kan horon jagoranci.

A bisa ka’idar yarjejeniyar, kowace Kungiyar za ta nada wanda zai yi aiki a hukumance wanda zai rika gudanar da ayyukan kowace kungiya domin gudanar da aikin.

A cikin sharuɗɗan fahimtar juna tsakaninsu, AMDF za ta ba da ƙwarewar da ake bukata a cikin tsarawa da aiwatar da horon.

Da take mayar da martani bayan sanya hannu kan takardar, shugabar cibiyar Kungiyar NUJ, Asma’u Yawo Halilu ta bayyana cewa sanya hannu kan yarjejeniyar na daga cikin alkawuran da ta yi na yakin neman Zaben ta.

“Wannan babbar nasara ce ga Kungiyar domin bayan horar da shugabannin kungiyar, za a zakulo mambobin kungiyar daga cibiyoyi daban-daban domin samun horon kwararru na lokaci zuwa lokaci har tsawon wa’adinmu”.

Haka kuma za a sake duba wa’adin yarjejeniyar da ake sa ran zai dore a tsawon wa’adin sabbin shugabannin a duk shekara don tabbatar da cikar manufarsa.

Sa hannu kan yarjejeniyar ya biyo bayan tayin da AMDF ta yi a ziyarar da ta kai kungiyar NUJ ta Kaduna a ranar 17 ga Disamba, 2021 bayan an rantsar da sabuwar gwamnatin Kungiyar a ofis din.

1 COMMENT

Leave a Reply