Kotu ta kama shugaban EFCC da laifi

1
309

Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta samu shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, Abdulrasheed Bawa da laifin saɓa wa umurnin kotu, a wani hukunci da ta yanke a 2018.

A hukuncin da ya yanke yau Talata, mai shari’a Chizoba Oji ya ce hukumar ta EFCC ta ƙi aiwatar da wani hukuncin da kotu ta yanke a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018, inda ta umurci hukumar da ta mayar wa wani mutum motarsa kirar Range Rover da kuɗi naira miliyan 40.

Kotun ta buƙaci da a tura shugaban hukumar ta EFCC gidan yari har sai ya wanke kansa daga laifin.

Haka nan kotun ta buƙaci sifeta janar na ƴan sandan Najeriya ya tabbatar an aiwatar da hukuncin.

Wanda hukuncin na shekarar 2018 ya buƙaci da a mayar wa kayan nasa ne ya shigar da ƙara, inda yake zargin hukumar da ƙin bin umurnin da kotu ta bayar a hukuncin na farko.

1 COMMENT

Leave a Reply