No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati EFCC AbdulRasheed Bawa ya ce ya ɗaukaka ƙara dangane da hukuncin da wata kotun birnin tarayya ta yanke masa ranar Talata a Abuja.

Kotun yanke hukuncin tura shi gidan yari sakamakon kama shi da laifin raina umarnin kotu.Tun da farko dai kotun ta umarci shugaban da ya mayar da wasu kudi da suka kai naira miliyan 40 da wata motar alfama da hukumar ta karba daga wani mutum da ta zarga da laifin rashawa.

Shugaban EFCCn ya ce shi a karan kansa bai yi watsi da umarnin kotun ba a matsayinsa na shugaban hukumar, ballantana ya fuskanci fushin kotu, saboda a saninsa kotun ta bayar da umarnin ne tun a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018. Wato shekara uku kenan kafin ya zama shugaban hukumar ta EFCC, dan haka ba shi aka bai wa umarnin ba kuma a cewarsa babu yadda za a yi laifin wani ya shafeshi.

KU KUMA KARANTA: <strong>Kotu ta kama shugaban EFCC da laifi</strong>

Ya ƙara da cewa ”Mun riga mun ɗaukaka ƙara game da wannan hukunci, dan haka za mu jira domin ganin yadda shari’ar za ta kasance”.

Amma ya ce duk da haka ya bayar da umarni a mayar da wannan motar alfarma ga mai ita tun a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekarar, tare da bayar da umarnin bin hanyar da ta dace wajen mayar da kuɗin naira miliyan 40 ga mai su.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...