Ko ka san su waye shaharararrun ‘yan dambe Shago da Ɗan Dunawa?
Shago da Ɗan Dunawa shahararrun ‘yan Damben Gargajiya ne da suka shahara a garin Gusau a shekarar 1957.
Shago da Ɗan Dunawa wasu shahararrun ‘yan dambe ne da aka yi a ƙasar Hausa, waɗanda suka sha karawa da juna har ta kai ga sun ɗauki alƙawarin ba za su ƙara wasan dambe da junan su ba.
Akwai lokachin da Ɗan Dunawa ya je Kano suka kara da Shago, yawancin mutane suna zaton Shago zai buge Ɗan Dunawa, amma sai lamari ya canza a inda Shagon ya sha wuya kamar yadda muka gani a jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo ta shekarar 1957.
KU KUMA KARANTA: Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya suyi taro a Kaduna
A cikin hoton za a ga Ɗan Dunawa a hannun hagu da Shago a hannun dama, da Malam Dogonyaro, wato shugaban direbobi na Gusau a tsakiyar hoton, sai makiɗin Ɗan Dunawa a hannun hagu riƙe da kotso.
Dukkansu sun rasu, Allah ya gafarta masu da dukkan musulmi baki ɗaya, Amin.









