Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya suyi taro a Kaduna

0
39
Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya suyi taro a Kaduna

Gwamnonin Jihohin Arewa 19 da Sarakunan Gargajiya suyi taro a Kaduna

Daga Idris Umar,Zariya

Gwamnonin jihohin Arewa guda 19 sun gudanar da muhimmin taro tare da manyan sarakunan gargajiya daga yankin Arewa, a wani yunkuri na fuskantar matsalolin tsaro, tattalin arziki, da ci gaban al’umma. Taron ya gudana a birnin Kaduna, karkashin jagorancin Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ke shugabantar kungiyar Gwamnonin Arewa.

KU KUMA KARANTA:Taron Gwamnonin Arewa Maso Gabas: Dole ne mu ƙarfafa haɗin kai don dakatar da matsalar tsaro – Gwamna Buni

Haka zalika, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, wanda shi ne shugaban majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya, ya kasance a sahun gaba wajen jagorantar bangaren sarakunan gargajiya a taron.

Taron ya kunshi tattaunawa kan hanyoyin da za a bi don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Arewa, da kuma hanyoyin karfafa hadin kai tsakanin gwamnoni da sarakunan gargajiya domin cimma burin ci gaban yankin gaba ɗaya.

Leave a Reply