Hukumar Kwastam Shiyyar Kano/Jigawa Ta Kama Fatun Jaki Na Sama Da Miliyan 416

0
271

Daga; Rabo Haladu, Kaduna.

HUKAMAR Hana Fasa-kwauri ta Kasa shiyyar Kano da Jigawa, ta bayyana cewa ta samu nasarar kama fatun jaki guda 3,712 wanda kudinsu ya kai sama da miliyan 416 da wasu haramtattun kaya.

Shugaban hukumar Kwantirola Mohammed Abubakar Umar, shi ne ya sanar da hakan lokacin da yake baje kolin kayan ga manema labarai a hedkwatar hukumar dake Kano.

Hakazalika, ya kara da cewa hukumar ta tara kudin haraji sama da Naira biliyan 10.1 a cikin watanni uku da ya yi da fara aiki a matsayinsa na Shugaban hukumar a shiyyar Kano da Jigawa.

Kwantirola MA Umar, ya bayyana cewa daga cikin kayayyakin da Hukumar Hana Fasa-kwauri ta shiyar Jihar Kano da Jigawa ta kaman, har da Fatun Jakunkuna da suka kai kimanin guda 3,712 wanda adadin kudinsu ya kai Naira 416,382,278 wanda aka yi kokarinn fita da su zuwa Kasar waje, sai kuma shinkafar waje mai nauyin kilo 50 guda 1,031 da fakitin taliyar waje guda 151 sai fakitin Macaroni guda 91.

Sauran kayan sun hada da, dilar gwanjo guda 131 da kuma shinkafar waje mai kilo 25 guda 3 da kuma sabulun wanki na waje guda fakiti 6.

Acewarsa, daga kama aikinsa zuwa yanzu hukumar ta samu nasarar kara tara kudin harajin da take samu inda ya ce a shekarar data gabata hukumar ta tara biliyan 7 amma daga zuwansa cikin watanni uku sun tara Naira biliyan 10 da doriya.

MA Umar, ya kara da cewa zasu ci gaba da lalubo hanyar da zasu kara inganta samun kudadan haraji ta hanyar yin aiki kafada da kafada da sauran bangarorin hukumar dake aiki a shiyyar.

Ya ce hakan ya samu ne bisa irin kwarin gwiwar da shugaban hukumar kwastan ta kasa Hameed Ali yake basu ne, yana mai cewa za su ci gaba da yin bakin kokarin su wajen tabbatar da cewa an hana fasa kwauri domin bunkasa ci gaba tattalin arzikin Najeriya baki daya.

Ya kara da cewa hukumar kwastan shiyyar Kano da Jigawa, ta himmatu wajen ganin ta dakile ayyukan masu fasa kwauri inda yace Jami’ansu suna aiki babu dare babu rana domin tabbatar da hakan.

Ya ce “za mu yi bakin kokarin mu wajen ganin munyi aiki da masu ruwa da tsaki a shiyyar wajen ganin hakarmu ta cimma ruwa akan samar da hanyoyin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa baki daya.”

A karshe, Kwantirolan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika kiyaye doka, domin ko kadan bai kamata a ci gaba da shigo da ire-iren wadannan kayayyaki da aka san gwamnati ta haramta shigowa da su ba.

Leave a Reply