Kaduna 2023: Dattijo Ya Fara Rangadin Ganawa Da Shugabannin Jam’iyyar APC

0
321

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

BIYO bayan sanarwar bayyana ra’ayin tsayawa takarar neman Gwamnan Jihar Kaduna da Muhammad Sani Abdullahi (Dattijo) ya yi a ranar talata, Dan takarar ya fara rangadin kwana biyu a kananan hukumomin Jihar domin ganawa da shugabannin Jam’iyyar APC da manyan masu ruwa da tsaki a unguwanni da kananan hukumomi domin neman goyon bayansu gabanin zaben fidda gwani na Jam’iyyar.

Tuni Dattijo da tawagarsa sun ziyarci kananan hukumomi bakwai dake cikin Shiyya ta daya wadanda suka hada da kananan hukumomin Lere, Kubau, Ikara da Soba a ranar Laraba.

Kuma a rana ta biyu, tawagar ta zagaya kananan hukumomin Sabon Gari, Kudan da Makarfi, a ranar Alhamis. Idan dai za a iya tunawa, a baya Dattijo ya gana da masu ruwa da tsaki daga karamar hukumar Zariya.

Yayin da tawagar Dattijo a Lere ta fara da ziyarar mai martaba Sarkin Lere, Injiniya Suleiman Umar Lere da Mai Martaba Sarkin Saminaka, Honarabul Muhammadu Sani, dukkansu sun yi masa addu’o’i da fatan alheri.

Da yake jawabi ga dimbin Jama’ar da suka tarbesu, Muhammad Sani Dattijo ya mika godiyarsa ga ‘ya’yan Jam’iyyar bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatin APC mai ci na tsawon shekaru.

Dattijo ya bukace al’ummar da su mara masa goyon baya a kan burinsa na ganin cewa ya kara karfafawa a kan nasarorin ayyukan da Gwamna Nasir El-Rufai ya ke yi.

Dattijo, ya kuma shawarci ‘ya’yan Jam’iyyar da su kasance masu hadin kai da biyayya ga Jam’iyyar da Gwamna Nasir El-Rufai.

A cewar Dattijo, akidar Jam’iyyar ta na sama kowa kuma fiye da muradin su, don haka dole ne kowane mamba ya kasance mai biyayya ga Jam’iyyar a karkashin jagorancin shugabansu Malam Nasir El-Rufai.

Shugabanni masu kishin Jam’iyyar da shugabannin Jam’iyyar da masu ruwa da tsaki daga matakin kananan hukumomi da na Unguwa a fadin kananan hukumomi 7 sun bayyana goyon bayansu ga muradin Muhammad Sani Dattijo.

Za a ci gaba da rangadin ne a mako mai zuwa tare da kai irin wannan ziyarar a wasu kananan hukumomin dake shiyyar ta biyu da ta uku na jihar Kaduna.

Leave a Reply