Gwamnatin Kaduna Ta Jaddada Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Tsakaninta Da Kungiyar NUJ Jihar

0
836

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

GWAMNATIN Jihar Kaduna ta jaddada shirinta na karfafa hadin gwiwa tare da kulla kyakkyawar alaka da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana hakan ne a jiya ta bakin babban mai baiwa gwamna Nasir El-Rufa’i shawara kan harkokin yada labarai da sadarwa a ziyarar da mambobin kungiyar NUJ ta Kaduna suka kai gidan gwamnati.

Mista Muyiwa Adekeye, babban mai ba gwamnan shawara na musamman ya bayyana cewa abin da gwamnati ta sa gaba shi ne ta tabbatar da an sanar da mutane isassun manufofin gwamnati da kuma ci gaban da gwamnati ke samu a Jihar.

Adekeye, yayin da yake jawabi ya yaba da kyawawan halaye da kuma rawar da kafafen yada labarai ke takawa wajen fadakar da jama’a game da abubuwan da ke faruwa a kusa da su da kuma inganta karfinsu ta hanyar musayar bayanai.

Kakakin ya kara da cewa gwamnatin jihar Kaduna a baya ta horas da jami’an hulda da jama’a (PROs) da daraktoci da sakatarorin dindindin na ma’aikatu da ‘yan jarida domin su rika sadarwa da manufofin gwamnati yadda ya kamata.

Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin Kaduna za ta rubanya kokarinta na ganin an dore da kyakkyawar alaka tsakanin Jihar da kungiyar.

Tun da farko, shugabar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, Kwamared Asma’u Yawo Halilu, ta baiwa Gwamnatin Jihar tabbacin bada cikakken goyon bayanta da hadin kan shugabancinta ta hanyar ganin cewa an bunkasa aikin Jaridar.

Ta ce, Kungiyar ba za ta lamunci ta kowace fuska ta goyi bayan aikin jarida na son zuciya, rashin adalci da labaran karya ba.

Leave a Reply