Mahara Sun Kaiwa Dan Majalisar Wakilai Na Mazabar Jos Da Bassa Hari

0
242

Daga; Isah Ahmed, Jos.

WASU mahara dauke da bindigogi, da ba a gane ko su waye ba, sun kai wa tawagar Dan majalisar wakilai ta tarayya, na mazabar Jos ta Arewa da Bassa da ke Jihar Filato, Honarabul Musa Agah hari a daren Talata, a inda suka hallaka mutum biyu, a cikin tawagar.

Su dai wadannan mahara sun kaiwa tawagar Dan majalisar hari ne, a lokacin da suke dawowa zuwa gida daga gaisuwar godiya da bangajiya kan zaben da aka yi masa a kwanakin baya, da ya kai wa al’ummar mazabarsa na yankin Miango da ke Karamar Hukumar Bassa, a inda abin ya faru a hanyar Miango da misalin karfe 9 na dare.

Da yake tabbatar da faruwar wannan al’amari, wani mataimaki na musamman ga Dan majalisar, kuma wanda abin ya faru kan idonsa, mai suna Moses Mali ya bayyana cewa a lokacin da wannan al’amari ya faru, Dan majalisar yana tare da matarsa da kananan ‘yayansa guda biyu, amma Allah ya kubutar da su ba tare da jin wani rauni ba, a lokacin da maharan suka bude masu wuta da harsasai.

Moses Maly, ya ce amma maharan sun hallaka shugaban jam’iyyar PDP na mazabar da shugabar mata ta mazabar, wadanda suke biye da tawagar a kan babur a lokacin.

Shi dai Honarabul Musa Agah, an rantsan da shi ne a kwanakin baya, bayan da ya lashe zaven cike gurbi na kujerar majalisar wakilai ta tarayya ta mazabar Jos ta Arewa da Bassa, da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabarairun da ya gabata, a karkashin Jam’iyyar PDP.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato, ASP Ubar Gabreal ta waya, kan wannan al’amari amma bai same shi ba.

Leave a Reply