Gandun Dajin Kamuku wani wurin Yawon Buɗe Ido ne, na gwamnatin tarayyar Najeriya a jihar Kaduna, da ke Arewa maso yammacin ƙasar.
Gandun Dajin, na da faɗin ƙasa kusan kilomita 1,120 (sq mi 430).
Har ila yau, wurin ya kasance a yammacin jihar Kaduna, kuma ya na kusa da gandun dajin Kuyambana zuwa arewa maso yamma mai nisan kilomita 14 daga babban birnin jihar.
KU KUMA KARANTA: Matsirga Waterfalls, Kaduna, Najeriya
An kafa Gandun Dajin ne a shekarar Alif da Ɗari Tara da Talatin da Shida (1936), a matsayin gandun dajin Birnin Gwari a ƙarƙashin gwamnatin Arewacin Najeriya.
An inganta shi daga wurin ajiyar namun daji na jiha zuwa gandun dajin ƙasa a watan Mayun Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Tara (1999), a wani ɓangare saboda nasarar da aka samu na wani aiki na al’umma da ke inganta amfani da albarkatu mai ɗorewa, wadda Savanna Conservation Nigeria, wata ƙungiya mai zaman kanta ta ƙasa ke gudanarwa.
Gwamnatin Tarayya ta kasance ta na neman haɗin guiwa tare da masu saka hannun jari na ƙasashen waje don haɓaka yawon buɗe ido a cikin wannan da sauran wuraren shaƙatawa na ƙasa.
Akwai aƙalla nau’ikan tsuntsaye guda 177, sannan akwai tarin Dabbobi waɗanda suka haɗa da, Giwaye, Birai, Jakin Dawa, Raƙumin Dawa, Bareyi, Kuregu, da wasu dabbobi waɗanda babu su a sassan Najeriya.
Al’ummar Kamuku
Sun kasance manoman gargajiya, mafarauta, makiyaya da masu sana’a, waɗanda aka san su da saƙa, yin tabarma da tukwane.
An ce al’ummar Birnin Gwari, sun samo asali ne daga garin Zungeru na jihar Neja, kuma an ce Kamuku sun fito ne daga yankunan Sakkwato da Katsina a lokacin jihadin Fulani a farkon ƙarni na 19.
Wurin shaƙatawan ya haɗa da wuraren da waɗannan mutane ke ɗaukan tsarki, kamar tuddai, tsaunukan duwatsu, da ƙoramu, da tsohon wurin bautar Parnono.
Garin Birnin Gwari na yanzu an kafa shi ne a cikin shekara ta Alif da Ɗari Tara da Hamsin da Bakwai (1957), daga mutanen Gwari waɗanda suka yi ƙaura daga wani ƙauye na farko da suka yi ƙaura, daga wani ƙauye mai kusan kilomita hamsin (31 mi) zuwa arewa.
Farauta da kiwo ba bisa ƙa’ida ba daga matsugunan makiyaya da ke gefen dajin na haifar da barazana ga muhallin dajin a halin yanzu.