FIFA ta sanar da filin da za a yi wasan ƙarshe na gasar Cin Kofin Duniya

0
166

Hukumar FIFA ta tabbatar da cewa za a buga wasan ƙarshe na Wasan Cin Kofin Duniya a filin wasa na MetLife a New Jersey/New York a ranar 19 ga watan Yulin 2026.

“Za a ɗaga kofin #FIFAWorldCup a New York New Jersey!” kamar yadda FIFA ta sanar a shafinta na X.

“ Za a gudanar da wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya na shekarar 2026 a New York New Jersey a ranar 19 ga watan Yulin 2026!”

Filin wasan na MetLife mai ɗaukar mutum 82,500 shi ne filin da ƙungiyar New York Jets da New York Giants ke atisaye, haka kuma a filin ne aka buga wasan ƙarshe na Copa America inda ƙasar Chile ta doke Argentina.

FIFA ta ce za a buɗe wasan ne a filin wasa na Estadio Azteca da ke birnin Mexico a ranar 11 ga watan Yuni. Haka kuma ta ce za a buga wasan samun gurbi na uku a filin wasa na Hard Rock da ke Miami Gardens a Jihar Florida.

KU KUMA KARANTA: Mbappe ya zama mafi girman kima na FIFA 23 tare da jimlar 92

Gasar Cin Kofin Duniya karo na 23 za ta kasance ta farko wadda za a gudanar da ita a ƙasashe uku waɗanda suka haɗa da Canada da Mexico da Amurka.

Gasar wadda a karon farko ƙasashe 48 za su buga za a yi wasanni a filayen wasa 16 a faɗin jihohin Amurka waɗanda suka haɗa da New York da Dallas da Miami da Kansas da Houston da Atlanta da Los Angeles da Philadelphia da Seattle da San Francisco da Boston.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here