EFCC ta kama manyan motoci 12 da mutum 41 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

0
102

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati EFCC ta ce ta kama wasu manyan motoci 12 da wasu mutane 41 da ake zarginsu da hannu wajen haƙo ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma mallakar wasu ma’adanai daban-daban ba tare da lasisin da ya dace ba.

A sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na X ranar Laraba ta ce ta yi kamen ne a ranar Litinin 5 ga watan Fabrairun 2024 a wurare daban-daban da suka haɗa da Banni da Lade, Patigi da Okolowo a jihar Kwara, da kuma Igbeti da Ogbomosho a jihar Oyo.

“An yi nasarar kama su ne bayan samun sahihan bayanai a kan ayyukan da masu haƙar ma’adanai ba bisa ƙai’da ba ke yi, inda suke loda ma’adanai a cikin manyan motoci suna fita da su daga jihar ba tare da lasisin hukumomi ba,” in ji sanarwar.

EFCC ta bayyana sunan mutum 25 daga cikin mutanen da ta kama ɗin.

KU KUMA KARANTA: Shugaban EFCC yayi gargaɗi da jan hankali ga jami’an hukumar

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

Ko a watan Yulin 2023 ma sai da hukumar ta samu nasarar kama wani ɗan ƙasar China Gang Deng tare da ƙwace wasu manyan motocinsa biyu dauke da ma’adinan gwamnatin tarayya.

Sannan ta sake kama wasu ‘yan ƙasar China 13 da suka haɗa da mace daya da maza 12 bisa laifukan da suka shafi ƙetare iyaka kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply