Labarin yana gefen ku!

Shugaban EFCC yayi gargaɗi da jan hankali ga jami’an hukumar

1

Shugaban Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Tu’annati ta EFCC, Ola Olukoyede, ya buƙaci Jami’an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da su bi doka wajen gudanar da kame.

Olukoyede ya bayyana hakan ne a cikin Jawabinsa na sabuwar shekara ga Ma’aikatan Hukumar wanda aka wallafa a Dandalin Sadarwa na manhajar X wato Twitter na hukumar mai yaƙi da almundahana.

A cewarsa babu wata hukuma a Najeriya da ke da matuƙar muhimmanci ga ci gaban Najeriya kamar hukumar EFCC.

Don haka ya sha alwashin samar da hanyoyin da za su baiwa hukumar damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na yaƙi da cin hanci da rashawa a kasar.

Olukoyede ya kuma bayyana cewa, daga yanzu za a rika gudanar da kame da bada beli kamar yadda doka ta tanada.

KU KUMA KARANTA: EFCC ta titsiye Akanta-Janar tare da gayyatar ma’aikatan ofishin Betta Edu

Babban maƙasudin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran laifuffukan da suka shafi kuɗi shi ne, samar da ci gaban tattalin arziki da samar da wadata da guraben ayyukan yi ga Jama’a.

“Ya kamata mu bankado hakikanin gaskiya, mu yi aiki da su, al’ummarmu na cikin mawuyacin hali, muna bukatar mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa don ƙara samar da kuɗaɗen shiga daga wasu tsirarun bara gurbi ga Najeriya”.

Babu wata hukumar gwamnati da ke da matukar muhimmanci ga ci gaban al’ummar kasa kamar hukumar EFCC Muna da duk abin da ya kamata don kawo bayanin martaba da ƙididdiga na ci gaban al’ummarmu.

Bari in kuma yi magana game da bitar ka’idojin kame da kuma bada beli wanda nake sa ran kowa ya sani a yanzu.

“An sanar da bitar ne da bukatar mu bi kyawawan ayyuka na kasa da kasa wajen aiwatar da doka, “Mu jami’an tsaro ne na yaƙi da cin hanci da rashawa, kame da beli duk a yanzu za su kasance daidai da tsarin doka, ya kamata masu binciken mu su lura da wannan.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.