Dokta Suleiman Shinkafi Ya Kai Ziyara Ofishin Jakadancin Kasar Dubai

0
334

Daga; IMRANA ABDULLAHI.

AKOKARIN da yake na ganin Jihar Zamfara ta samu karbuwa a idanun duniya domin amfanuwa da abubuwa da suka hada da bangaren tsaro, Kiwon lafiya, Ilimin addini domin ganin Jihar Zamfara ta yi fice har ta tsarewa tsara.

Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara Shawara a kan hulda da yarjejeniya da kasashen duniya Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi na farko, ya kai ziyarar hada kyakkyawar dangantaka tsakanin Jihar Zamfara da babban ofishin jakadancin hadaddiyar Daular larabawa “Dubai” da ke birnin tarayya Abuja.

A ziyarar dai an samu damar tattauna hada kyakkyawar dangantaka tsakanin hadaddiyar Daular Larabawa da Jihar Zamfara mai dimbin albarka.

“Yayin ziyarar an samu tattauna mahimman batutuwan ci gaban Jihar Zamfara, wakilin jakadan kasar Dubai da ke Najeriya ya ba da tabbacin ganin sun kulla kyakykyawar dangantaka da Jihar Zamfara”.

Tun da farko da yake jawabi a lokacin ziyarar mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan harkokin hulda da kuma yarjejeniya da kasashen duniya Honarabul Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, kira ya yi ga kasar hadaddiyar daular ta Larabawa “Dubai” da ta taimakawa Jihar Zamfara ta fannin Ilimin addini,Lafiya da batun tsaro kasancewar Jihar na fama da matsalolin tsaro a lokaci mai tsawo.

Ofishin jakadancin ya kuma yi alkawarin bayar da taimakon da yakamata kuma ya bayyana aniyarsu na yin ido da ido da Gwamnan Jihar Zamfara Dokta Bello Muhammad Matawalle domin tattaunawa a kan yadda za a gudanar da al’amuran.

Kamar yadda muka samu bayanan mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara ya kuma shiga wani taron tattaunawa na sirri a ofishin jakadancin duk da nufin lalubo hanyoyin warware bakin zaren ta yadda Jihar za ta amfana.

Ziyarar dai za ta ba Jihar Zamfara damar samun inganta wadansu abubuwa da ake bukatar bunkasasu.

Leave a Reply