Kwarewa Da Dadewar Emily Osuji Yasa Mu Amincewa Tabbatar Da Ita – Sanata Uba Sani

0
405

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

SANATA Uba Sani wanda yake wakiltar mazabar Jihar Kaduna ta tsakiya, ya bayyana amincewarsu na tabbatar da Uwar-gida Emily Osuji wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turo domin tantancewa a matsayin sabuwar shugabar ma’aikatar NDIC ta kasa, sakamakon kwarewarta da Dadewar a ma’aikatar.

A wani zantawa da manema labarai jim kadan bayan zaman tantancewar a zauren majalisar, Sanata Uba Sani ya yi karin haske game da lamarin Inda ya ce Uwar-gida Emily Osuji ta cancanta da matsayin kasancewar duk tsawon rayuwarta na aiki a nan ta yi su.

Ya ce “Uwar-gida Emily ta samu akalla shekaru 32 tana aiki a wannan ma’aikata wanda hakan muke ganin ya bata duk wata dama na cancantar zama sabuwar shugabar ma’aikatar NDIC, shi yasa ba mu tsaya yi mata wasu tambayoyi ba, kai tsaye muka amince da kudirin shi shugaban kasa Muhammadu Buhari na tabbatar da ita.”

“Toh kamar yadda aka sani, dokar ita wannan ma’aikata ta NDIC ta bada damar a duk lokacin da wani ko wata sukayi murabus daga wannan matsayin, wajibi ne a nemo wani ko wata a maye gurbin wannan mutumin don haka yasa a yanzu muka gudanar da wannan aikin, kuma cikin ikon Allah mun gama shi lami lafiya.”

“Kuma ga dukkan alamu, ita wannan mata daga ganin takardun ta, alamu sun nuna cewa kwarewarta da gogewa da dadewa sun tabbatar da cewar zata taimaka wa ita wannan ma’aikata da zata kawo ci gaba mai amfani, hakan yasa ni da abokan aikina ba tsaya yi mata wasu tambayoyi ba muka amince da tabbatar da ita kai tsaye.”

A karshe, Sanata Uba Sani wanda yake shi ne Shugaban Kwamitin Banki, Inshora da sauran Cibiyoyin Kudi, ya yiwa Uwar-gida Emily Osuji fatan alheri na ganin cewa an samu karin nasarori ta fannin samun tattalin arzikin kasa a karkashin Jagorancin ta.

Leave a Reply