Cika Shekara Daya Kan Mulki: Al’ummar Bichi Sun Yabawa Dokta Sabo

0
269

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

Al’UMMAR Karamar hukumar Bichi sun jinjinawa Shugaban Karamar hukumar, Dokta Yusuf Mohammed Sabo, Saboda kokarin da ya yi na samar da ci gaba mai albarka a wannan yanki Mai mazabu 11.

A cikin wata tattaunawa da wakilin mu ya yi da wasu daga cikin mutanen yankin, sun sanar da cewa ko shakka babu Dokta Sabo yana bakin kokarin sa wajen ganin yankin yana Kara bunkasa duk da irin halin da ake ciki na tattalin arziki a duniya baki daya.

Da yake zantawa da Gaskiya Tafi Kwabo a mazabar Saye, Malam Ahmadu Musa ya bayyana cewa a shekara daya kacal, Dokta Yusuf Mohammed Sabo yayi abubuwa masu matukar muhimmanci ga al’umar karamar hukumar Bichi bisa la’akari da bukatun al’umar kowane bangare.

Shima a nasa bangaren, wani matashi daga mazabar Badume Lawan Ahmed ya nunar da cewa Dokta Sabo mutum ne Mai kishin al’umar sa, sannan baya nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi aiki yake yi da gaske a matsayin sa na shugaba don haka nema aka Sami nasarori masu tarin yawa cikin shekara guda.

Haka kuma malama Hadiza Umar daga Bankaurar Saye tace a gwamnatin Dokta Yusuf Mohammed Sabo ba’a bar Mata a baya ba, ana sanya su cikin shirye-shiryen gwamnati Wanda hakan ke nuni da cewa nan gaba kadan kowa zai sami abin dogaro dakai saboda yadda zamani ke canzawa.

Dukkanin wadanda wakilin namu ya tattauna dasu sun yi godiya ga shugaba Dokta Sabo bisa namijin kokarin da yake yi wajen kyautata rayuwar al’uma da ingantaccen zamantakewa cikin shekara guda da yayi yana mulkin Karamar hukumar Bichi.

Leave a Reply