Daliban Madarasatul Hayatuddeen Islamiyya Gudau-Jola 14 Sun Yi Saukar Al-Qur’ani

0
301

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

A RANAR lahadin data gabata ne, makarantar Hayatuddeen Islamiyya dake garin Gudau-Jola ta yi Bikin saukar karatun Al-Qur’ani na dalubai sha hudu watau maza 7, mata 7 a wani kasaitaccen biki da aka gudanar.

An kafa wannan makaranta a Shekara ta 1992 da dalubai 13, malamai 2, yayin da yanzu makarantar tana da yawan dalubai maza da mata fiye da 600 wadanda kuma suna karatu cikin nasara.

Haka kuma an gudanar da jawabai masu matukar amfani na jan hankalin dalubai tare da jan hankalin iyaye da masu rike da yara wajen baiwa yaran nasu damar yin karatu na addini da na zamani domin kasancewa al’umma nagari.

Shugaban hukumar makarantun kimiyya da fasaha na jihar Kano, Dokta Kabir Bello Dungurawa wanda shi ne ya kasance babban bako wajen wannan taro, ya yi dogon jawabi kan muhimmancin ilimi da tarbiyya, tare da yin horo ga dalubai da su tsaya suyi karatu ingantacce domin samun rayuwa mai kyau.

Bugu da Kari, dukkanin malamai da suka yi maganganu a wajen sun bukaci iyaye da su kara kokari wajen baiwa yaransu damar samun ilimi mai kyau domin ci gaba da gudanar da rayuwa mai albarka, tare da yabawa dukkanin wadanda suke da hannu wajen ganin an gudanar da wannan biki na saukar karatu cikin nasara.

Leave a Reply