Al’ummar Garin Gudau Sun Yaba Wa Gwamna Ganduje, Sun Nemi A Duba Batun Hanyar Su

0
376

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AL’UMMAR garin Gudau “A” wanda aka fi sani da (Jola) sun yabawa gwamnatin Jihar kano bisa jagorancin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, saboda kokarin da ya ke yi wajen gudanar da aiyukan raya kasa kuma masu inganci a fadin Jihar.

A cikin wani sakon barka da Sallah da suka aika wa Gwamna Ganduje, al’ummar garin na Gudau sun bayyana matukar jin dadin su dangane da irin ci gaban da Jihar kano ke samu a wannan gwamnati, wanda kuma a cewar su, Jihar kano ta zamo abar misali cikin sauran Jihohin kasarnan.

Bugu da kari, sun roki gwamnatin Jihar ta kano da majalisar karamar hukumar Dawakin Tofa da su hada hannu domin samar da hanya daga garin Dungurawa zuwa Gudau musamman ganin cewa akwai dumbin al’umma da garuruwa dake bin wannan hanya mai tsohon tarihi.

Sannan sun yi amfani da wannan dama wajen yin fatan alheri ga dukkanin shugabanni da masu ruwa da tsaki na wannan yanki saboda gagarumar gudummawar da suke bayarwa wajen ci gaban wannan karamar hukuma ta Dawakin Tofa.

A karshe al’ummar garin Gudau sun isar da sakon barka da Sallah ga gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, wakilin karamar hukumar Dawakin Tofa a majalisar dokokin jihar kano, Saleh Marke, Shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa, Alhaji Ado Tambai Kwa, shugaban kwalejin fasaha na Jihar kano, Dokta Kabiru Bello Dungurawa, kwamishinan ayyuka, Idris Wada Saleh da kuma kansilan mazabar Gargari Abdullahi Yahaya Dungurawa.

Leave a Reply