‘Yan bindiga sun kai hari kurkukun Kuje

0
591

A yanzu haka ana jin harbe-harben bindiga a Kuje, birnin tarayyar Abuja, inda ake tsammani ‘yan bindiga sun kai hare a gidan kurkuku ne. Ban da ƙarar bindiga har da masu kama da boma-bomai ma ake ji.

An fara jin wannan kamar awa guda ne da ta wuce.

Gidan yarin Kuje dai yana ɗauke da manya-manyan mutane da gwamnati ke wa Shari’a kame su Abdul Rashid Maina da Mataimakin Kwamishina ‘yan sanda, Abba Kyari.

Maharan da suka zo a kan babura, a cewar wani da bai so Neptune Prime Hausa ta faɗi sunan sa ba, su so su shiga kurkukun ne ta baya amma masu tsaron ta suka yi turjiya kamun sojojin ruwa da ke Pegi su kawo musu ɗauki..

Leave a Reply