A yafemin, ban san Ahmad Gulak na kashe ba

0
308

A shekarar 2021, mai taimakawa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wato Ahmad Gulak, ya rasa ransa. An kashe shi ne a jihar Imo, bayan wasu ‘yan ta’adda sun gano inda yake a wani Otel, suka tari gaban motar shi a hanyar shi ta zuwa filin jirgi.

A bidiyon da wani Joe Iggbokwe ya sa a Facebook, ɗaya daga cikin wanda ake zargi da kashe Ahmad Gulak yayi bayanin yadda suka kashe shi, amma ya ne mi a yafe mishi.

A cewar shi, sun fita farautar mutane ne da abokanan aikin sa, inda suka ce ya bi gaban motar Gulak ya tare.

Danna wannan link don ganin cikakken bidiyon.https://fb.watch/e4lMhb1JyZ/

Suka ce mai ya fito, da fari yaƙi fitowa, sai daga bisani yafito, suka harbe shi amma harsashin bai ratsa jikin shi ba.

Yace mutumin nada rigar dake kare harsashi shiga jikin shi, se bayan ya cire ne, suka ƙara harbeshi har ya mutu. Sai bayan da suka kashe shi ya gane Ahmad Gulak suka kashe.

Daga bisani, suka tafi ƙona ofisoshin ‘yan sanda. Yace yana neman gafara a yafe mishi, yanzu ya gane aikin ta’addanci bazai kai shi ko ina ba.

Leave a Reply