An sace sojan ruwa mazaunin abuja, a jihar kogi

0
225

Daga Fatima Abubakar MONJA, Abuja

Wasu mutane wanda ba a sansu ba, sun sace ma’aikaci sojan ruwa da ke aiki da helkwatan sojojin ruwa dake Abuja, Mista Lawal Musa.

An sace shi ne a a garin lokoja, a cikin gidan shi dake bayan Flood Housing Estate, da misalin karfe 8 na dare a ranar litinin.

Wadan da ake zargi da sace Mr lawal dai sunyi nasarar shiga gidan shi ne ta hanyar lalata ƙofa da tagogin gidan.

Ma’aikacin zai tashi zuwa sabon wajen aikin shi ranar talata kafin abin tsausayin ya faru.

Bayan awa daya da faruwan lamarin, wadanda ake zargi da sace Mr lawal suka kira waya suna buqatan miliyan 3 kudin fansa.

Mai dakin Mr lawal dake bada labarin yadda abin ya kasance tace yan taaddan sun yankewa wa mijin nata hannu kafin suka tafi da shi cikin jini.

Leave a Reply