Wanda yayi tattakin shekara uku daga Afrika ta Kudu zuwa Makkah

0
287

Daga Fatima Abubakar MONJA, Abuja

Wani bawan Allah, me suna Sahid, yayi tattaki daga Cape town a ƙasar Afrika ta Kudu, zuwa ƙasa mai tsarki, Saudi Arebiya, inda yayi shekaru uku cif a hanya.

Ya shaidama manema labarai cewa ya fara tattakin shi na niyyan zuwa hajji a ranan 30 ga watan Ogusta, 2018 ta ƙasar Zimbabwe, Tanzaniya, Kanya, Sudan, Misra, sai ya ɓullah Falastin, inda annobar Korona ta tirsasashi tsayawa sakamakon an rufe boda.

Danna Wannan mahada don jin cikakken hirar: https://youtu.be/eW_ywHcVl6E

Sahid yace ya tsaya a Falastin fiye da shekara kafin a kuma bude boda, daga bisani ya cigaba da tafiya zuwa ƙasar Jodan, sai Madina kafin ya ƙarasa ƙasa mai tsarki, Makkah.

Leave a Reply