Chelsea ta sayi Sterling daga Man City

0
240

Chelsea ta tabbatar da kammala daukar dan kwallon Ingila, Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50.

Sterling, mai shekara 27, ya saka hannu kan kwantiragin kaka biyar a Stamford Bridge.

Tun da sanyin safiya dan kwallon tawagar Ingila ya yi ban kwana da ‘yan wasa da ma’aikatan Etihad ta kafar sada zumunta.

”Na koma Manchester City ina da shekara 20. Yanzu ni cikakken mutun ne,” in ji Sterling.

”Zan dade ina tuna lashe kofi 11 a kaka bakwai a Etihad har tsawon rayuwata.

City ta dauki Sterling daga Liverpool kan fam miliyan 49 a 2015.

Ya kuma ci wa kungiyar Etihad kwallo 131 a wasa 339 da lashe Premier League hudu.

Leave a Reply