Chelsea ta kammala duba lafiyar Nkunku, Haaland ya so ya tafi Liverpool

1
330

An kammala duba lafiyar ɗan wasan RB Leipzig mai shekara 24 asalin Faransa Christopher Nkunku wanda ke shirin tafiya Chelsea kan fam miliyan 52 a kasuwar ‘yan wasa ta kaka mai zuwa. (Bild)

Ɗan wasan Manchester City na Norway, Erling Haaland, mai shekara 22, ya so ya tafi Liverpool kafin rufe kasuwar ‘yan wasa, da ta gabata, amma daman Manchester United ba ta cikin tsarina. (Star)

Aston Villa  na nazari kan tsohon kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino da na Villarreal Unai Emery yayin da ake yada jita-jita kan makomar Steven Gerrard. (Football Insider)

Ɗan wasan gaba a Arsenal da Brazil Gabriel Jesus ya ce yana bukatar sauyi kan salon Pep Guardiola a Manchester City don haka yanzu jinsa yake hankali kwance karkashin Mikel Arteta. (ESPN)

Darakta a Paris St-Germain Luis Campos ya ce kungiyar ta yi kuskure wajen cimma yarjejeniya da ɗan wasan gaba na Brazil Neymar mai shekara 30 da Kylian Mbappe mai shekera 23 na Faransa.(Mail)

Tottenham na zawarcin dan wasan Leicester City, James Maddison, mai shekara 25 da ke buga wa Ingila tsakiya.(Football Insider)

Sabon kocin Chelsea Graham Potter na son bai wa Christian Pulisic mai shekara 24 ɗan kasar Amurka damar inganta kansa a Stamford Bridge kafin ya yanke hukunci kan makomarsa. (90min)

Potter bai rufe kofa ga dan wasan Belgium, Romelu Lukaku ba, na iya komawa Chelsea idan ya kawo karshen zaman da yake na aro a Inter Milan, ana sa ran a tattauna da dan wasan mai shekara 29 a karshen wannan kaka.(ESPN)

Kocin Aston Villa, Steven Gerrard ya ce Douglas Luiz, mai shekera 24, bai nuna alamun yana son sanya hannu a sabon kwantiragi da kulob din ba, batun da ke iya bai wa Arsenal damar cimma burinta kan dan wasan Brazil din mai buga tsakiya.

Ɗan wasan Juventus da Italiya Manuel Locatelli na iya barin kungiyar ta Serie A a kasuwar ‘yan wasa ta watan Janairu, kuma Arsenal ta nuna zawarcinta kan matashin mai shekara 24. (Calciomercato – in Italian)

Mai buga wa Wolves da kuma kasar Portugal Ruben Neves, dan shekera 25, ya yi watsi da tayin Manchester United da Liverpool a wannan kaka. (Sport – in Spanish)

Dan bayan Faransa William Saliba na azarbabin sanya hannu a sabon kwantiragi da Arsenel, yayin da yake samun tayi daga kungiyoyi da dama da ke farautar matashin dan shekara 21. (Five Insider)

Dan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 25, na cikin jeren sunayen ‘yan wasan da Manchester United ke farauta a kaka mai zuwa.(ESPN)

Chelsea ta sanya sunan babban jami’in RB Leipzig Christopher Vivell cikin kwararrun ma’aikata da take son dauka a Stamford Bridge. (Standard)

Real Madrid na shirin mika tayi ga ɗan wasan Brazil Eder Militao, mai shekara 24, domin tsawaita kwantiraginsa zuwa 2028. (Fabrizio Romano)

1 COMMENT

Leave a Reply