Bola Ahmad Tinubu Shi Ya Fi Cancanta Da Gadar Shugaba Buhari – Inji Abdullahi Kabir

0
309

Daga; Sani Gazas Chinade, Damaturu.

A TATTAUNAWAR da gidan Jaridar Gaskiya Tafi Kwabo (GTK) ta yi da wani matashi kuma kusa a jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan a garin Azare cikin karamar hukumar Karagum a Jihar Bauchi, Malam Abdullahi Kabir, dangane da danbarwar da ake kokarin farawa na lalubo wanda zai maye gurbin Shugaba Buhari idan wa’adin sa na barin mulki ya cika a shekara mai kamawa ta 2023 in rai ya kai, matashin ya fito karara ya bayyana cewar a ganinsa babu wanda ya ke ga ya cancanta da gadar shugaba Buhari fiye da jagoran jam’iyyar APC na kasa tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmad Tinubu. Asha karatu lafiya.

GTK: Muna so ka dan tsakurowa masu karatu tarihin ka a takaice?

Abdullahi:- To ni dai Suna na Abdullahi Kabir, ni dan Jam’iyyar APC ne daga Azare karamar hukumar katagum dake Jihar Bauchi. A baya na yi takarar kujerar dan majalisar dokoki mai wakiltar mazabar Azare/Madangala a 2015, kana na zama mamba na kungiyar Buhari Organization tun daga 2002 zuwa 2007 tare kuma da rike mukamin CPC Awareness Forum.

Baya ga haka kuma na rike mukamin sakataren Jihar Bauchi na kungiyar Nigeria Consolidation Ambassadors Network (NCAN) kungiyar da suka sayawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Form na tsayawa takarar Shugaban Kasa a 2019. Hakazalika na zama mamba na presidential campaign council a bangaren field operation duka dai a shekarar ta 2019. A Takaice ke nan.

GTK: Toh kasantuwar gashi wa’adin mulkin Shugaban Buhari ya kusa kaiwa karshe, shin wa kake ganin ya dace da gadonsa a wannan matsayi?

Abdullahi:- Alal hakika in aka lura da yadda shi Tinubu ya bada gudummawa wajen kaiwa ga nasarar shugaba Buhari da Jam’iyyar hadaka ta APC a zabukan 2015 da 2019 na ke ganin a daidai wannan lokaci babu wanda ya cancanta ya zama dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa 2023 da zai maye gurbin shugaba Buhari kamar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu Jagaban Burgu Jagoran Jam’iyyar APC na Kasa tsoron Gwamna Jihar Legas.

Dalilina na fadar hakan kuwa shi ne, shi Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya dade yana bada gudunmuwa mai tsoka a siyasar Najeriya tun ma kafin kafa Jam’iyyar mu ta APC domin ya kawo cigaba sosai a Jihar Legas a lokacin da ya ke Gwamnan Jihar Legas tare kuma da bunkasa tattalin arziki Jihar ta Legas ta hanyoyi da dama da suka hada da bunkasa hanyoyin kudin shiga ta yadda ba sai Jihar Legas ta dogara da kudeden da Gwamnatin tarayya ke bada wa ba. Sanin kowa ne Jihar Legas ita babban cibiyar kasuwanci ce a kasar Najeriya.

GTK:- A matsayin ka na dan Arewa, ko kana ga yankin ka ya amfana da gudummwar Tinubu?

Abdullahi:- Kwarai da gaske yankin mu na Arewa ya amfana da gudummawar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ta fuskoki da dama kuwa da suka hada da: Goya baya ga dan Arewa don ganin mulkin kasa ya dawo Arewa da karfin sa, Jama’arsa da dukiyar sa a yayin da Arewan ke da bukatar hakan a 2015.

“Ba nan ya tsaya ba har ila yau ya kuma bada gudumawarsa ga ‘yan Arewacin Najeriya a sauran zabukan 2007 da 2011 hade da zabukan shekarar 2015 da 2019 wadda hakan ne ya sake tabbatar mana cewar, lalle Tinubu masoyin Arewa ne na hakika wabda ke da bukatar mu saka masa.”

Kuma ma ai a zaben shekarar 2007 ya bawa tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar goyon baya a takarar sa da ya tsaya a Jam’iyyar AC ta Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, hakazalika a 2011 ya sake bada gagarumin gudummawa ga Malam Nuhu Ribadu a lokacin da ya tsaya takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar ACN a 2011. Asiwaju Bola Ahmad Tinubu bai gajiya ba sai dai ya bada gudunmuwa na kafa Jam’iyyar APC wanda a yau take jagorancin kasa.

Kuma Shi ne wanda ya soma tasowa tare da dukkan manyan jiga-jigan Jam’iyyar ACN zuwa garin kaduna don gabatar da tayin yin hadaka na jam’iyyun adawa don su hade guri daya don su tunkari Jam’iyyar PDP mai mulki a wancan lokacin aka kuma kai ga nasarar kamar yadda na fada a baya.

GTK:- Ko wace rawa gwanin naka ke takawa wajen tallafawa daidaikun al’umma?

Abdullahi:- A gaskiya a yanzu a sanina kaf ‘yan siyasar mu a Najeriya babu wanda ya kai shi gina mutane a siyasance, kuma babu wanda ya kai shi sanin yadda za a magance matsalolin mu na siyasa da ma wadda ba na siyasa ba kaman sa, tabbas idan ya zama dan takarar Shugaban Kasa ba zai yi wahalar tallatawa ba cikin sauki Jam’iyyar APC za ta samu gagarumin nasara na lashe zabe cikin kankanin lokaci kuwa wadda kan hakan ne ma a zancen da na ke yi a yanzu haka tuni na rubuta wani littafi a kan tarihinsa da gwagwarmayar sa da zan kaddamar da shi nan da ‘yan kwanakin nan a Arewa House a garin Kaduna Insha Allah.”

GTK:- Me ya jawo hankalin ka na rubuta wannan littafi a kan Asiwaju Bola Ahmad Tinubu?

Abdullahi:- A hakikanin gaskiya na rubuta wannan littafi nawa ne bisa lura da yadda ya bada gudumawarsa a fannoni da dama da suka hada da siyasa da ayyukan cigaban kasa da sauran su ya sa naga ya dace na rubuta littafi wanda ya kunshi nasarorin sa da gudumawar da ya bayar a siyasance saboda kada tarihi ya manta da shi.

“Kuma na yi nazari sosai a kai sannan na ga ya kamata na rubuta littafi a harshen Hausa don mutanen Arewacin Najeriya su fahimci waye Asiwaju Bola Ahmad Tinubu sosai kasancewar Arewacin Najeriya ita ce yankin da ya fi ko ina yawan al’umma mai dauke da Jihohi akalla 19 banda Abuja babban Birnin Tarayyar kasar nan.”

GTK: A matsayin ka na jigo a Jam’iyyar APC me za ka ce kan rikicin cikin gida wanda yanzu haka ya baibaiye Jam’iyyar ta ku ta APC?

Abdullahi: To a gaskiya ni a ganina wannan rikicin da yake faruwa a Jam’iyyar APC ba komai bane illa cikar Jam’iyya domin babu yadda Jam’iyya za ta cika sosai ba tare da samun matsaloli ba nan da can kasancewar in dambu ya yi yawa baya jin mai, to amma duk da haka za a shawo kan matsalolin in Allah yaso wadda a karshe zai zama mana alheri.”

Leave a Reply