Connect with us

Siyasa

An Zabi Abdullahi Adamu Shugaban Jam’iyyar APC

Published

on

Daga Wakilinmu

Abdullahi Adamu

Wakilan jam’iyyar APC daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam’iyyar da ke mai mulkin kasar.

Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam’iyyar bayan duka waɗanda suke takara sun janye wa Abdullahi Adamu.

Sanata Abdullahi Adamu, wanda da farko ba ya cikin waɗanda suka nuna sha’awar takarar shugabancin APC, daga bisani ya kutso kuma ya samu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni.

Wannan goyon bayan ne ya tilasta wa sauran ƴan takarar shugabancin APC janye wa a ranar Asabar kafin shiga dandalin taron.

Ƴan takarar da suka janye sun da tsohon gwamnan Benue George Akume da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da tsohon gwamnan Zamfara Abdul’Aziz Yari Abubakar da Saliu Mustapha d kuma Etsu Muhammed.

Sanata Adamu ya zama sabon shugaban APC ne fiye da shekara guda bayan sauke tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole daga mukamin da kuma nada Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin riko na jam’iyyar.

Sanata Adamu tare da tsoffin shugabannin APC biyu ( Edo Adams Oshiomhole da John Oyegun
Bayanan hoto,Sanata Adamu tare da tsoffin shugabannin APC biyu ( Edo Adams Oshiomhole da John Oyegun

Abdullahi Adamu yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya kuma sau biyu yana zama gwamna a jihar ta Nasarawa.

Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarawa ne daga sekarar 1999 zuwa 2007. Hasalima shi ne gwamnan farar-hula na farko a jihar.

An haife shi a garin Keffi da ke jihar Nasarawa kuma ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a jihar Nasarawa da kuma Benue ta yanzu a daga 1960 zuwa 1962.

Ya kuma yi karatun gaba da Sakandare a Kwalejin Fasaha, Bukuru, da kuma Kwalejin Fasaha da ke Kaduna wato Kaduna Polytechnic inda ya samu Babbar Difiloma.

A shekarar 1992, ya kammala Digirinsa na farko a fannin Lauya a Jami’ar Jos kuma ya zama lauya a 1993.

Sanata Adamu ya soma siyasa a 1977, kuma ya rike mukamai da dama.

Ga abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabon shugaban jam’iyyar APC:

  • Yana cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a 1998 wadda ta mulki Najeriya tsawon shekara 16
  • Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarwa na farar-hula na farko daga 1999 2007 a karkashin jam’iyyar PDP. Bayan ya kammala wa’adinsa na gwamna, an zabi Abdullahi Adamu a matsayin Sakataren Kwamitin Amintattu na PDP.
  • Shi ne shugaban farko na kungiyar gwamnonin Najeriya daga 1999 zuwa 2004.
  • Ya fita daga PDP a 2013 inda ya shiga jam’iyyar APC kasa da shekara daya bayan kafa ta. Yana cikin mambobin Sabuwar PDP da suka narke suka kafa APC.
  • Ya zama Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya
  • A shekarar 2010, hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najerita ta’annati ta zari Abdullahi Adamu da mutum 18 da yin zambar N15 bn.

Gabanin babban taron jam’iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya shaida mana cewa ba ya tsoron fafatawa da kowanne dan takara a zaben shugabancin jam’iyyar yana mai cewa “ban taba faduwa zabe ba don haka ba na shakkar kowa”.

Ya ce a matsayin sa na mutumin da ya jagoranci kwamitin sulhu na jam’iyyar, shi ne ya fi sanin kalubalen da ke gaban jam’iyyar da kuma yadda za a shawo kansu.

Sai dai masu sharhi a kan harkokin siyasa na cewa akwai babban kalubale a gaban tsohon gwamnan na jihar Nasarawa ganin yadda ake zargin cewa wasu daga cikin ‘yan takarar sun amince su yi maslaha ne kawai saboda babu yadda za su yi.

Baya ga haka, jam’iyyar ta APC na fuskantar babban kalubale a zaben 2023 sakamakon zargin da wasu ‘yan kasar ke yi cewa ba ta cika galibin alkawuran da ta daukar musu ba, ko da yake jam’iyyar ta sha cewa tana bakin kokarinta.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Published

on

APC ta dakatar da ɗan Majalisa kan cin amana a Zamfara

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta dakatar da Ɗan Majalisar Wakilai, Aminu Jaji bisa wasu zarge-zargen da ake yi masa na cin amanar jam’iyyar.

Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Malam Yusuf Idris ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Gusau a ranar Juma’a.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, Jaji yana wakiltar mazaɓar Ƙaura-Namoda/Birnin-Magaji a Majalisar Wakilai a ƙarƙashin jam’iyyar APC.

Idris ya ce wasu zarge-zargen da ake yi wa Ɗan Majalisar sun haɗa da aikata rashin gaskiya da rashin zuwa tarurrukan jam’iyyar da kuma sauran ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Kotun Najeriya ta bayar da umarnin dakatar da asusun banki fiye da dubu 1

Ya ce, matakin ya biyo bayan sanarwar dakatarwar da aka yi wa Jaji daga shugabannin jam’iyyar APC na mazaɓar Birnin-Magaji bisa zargin cin amanar jam’iyyar da dai sauran abubuwan da suka saɓa wa jam’iyyar.
Idris ya ce, “Kwamitin zartaswa na jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Birnin Magaji ne ya miƙa sanarwar dakatarwar zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar.

Bayanai sun ce kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na jihar ya gudanar da taron gaggawa a sakatariyar jam’iyyar da ke Gusau a ranar Juma’a 17 ga watan Mayu, 2024, inda aka gabatar da batun dakatar da Jaji ga ‘yan majalisar zartarwar jihar.

Continue Reading

Labarai

Tsohon gwamnan Katsina, Shema ya sauya sheƙa zuwa APC

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, a hukumance ya koma jam’iyyar APC Mai mulki a jihar.

Shema, ya kasance gwamnan jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan ya yi rajista ne a ofishin jam’iyyar na mazaɓar Shema, ƙaramar hukumar Dutsin-ma, inda shugaban jam’iyyar na jihar, Sani Aliyu-Daura ya ba shi katin zama ɗan jam’iyyar APC.

Lambar katin Shema ta zama ɗan jam’iyyar ita ce: 26551.

KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Yobe za ta mayar da kwale-kwalen Dufuna mai shekaru 8,000 zuwa cibiyar yawon buɗe ido

Malam Aliyu-Daura ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa da kuma tsohon gwamnan jihar Aminu Masari wanda ya gada, a bisa rawar da suka taka wajen ganin Shema ya sauya sheƙa.

Don haka ya tabbatar wa tsohon gwamnan cewa za a yi masa adalci kamar kowane ɗan jam’iyya.

Shugaban ma’aikata na Raɗɗa, Jabiru Abdullahi-Tasuri, shi ne ya miƙa katin zama ɗan jam’iyya ga Shema a madadin gwamnan a jiya Alhamis a Dutsin-ma.

Continue Reading

Labarai

Fusatattun matasa sun lakaɗawa kwamishina duka a wajen zaɓen fidda gwani

Published

on

Banji Ajaka, kwamishinan lafiya na jihar Ondo, ya gamu da fushin matasa a jiya Asabar yayin da ake gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC mai mulki a jihar.

Daily Trust ta gano cewa Dakta Ajaka, wanda ke Mazaɓar Ugbo 3, a ƙaramar hukumar, ana zarginsa da ɓoye takardar sakamakon zaɓen.

Shaidu sun tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da suka yi da manema labarai, inda suka yi zargin cewa fusatattaun matasan ‘ya’yan jam’iyyar APC ne da ke adawa da tsarin da aka bi wajen gudanar da zaɓen.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida lamarin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa rikicin ya faro ne lokacin da ‘yan ɗaya ɓangaren na jam’iyyar suka buƙaci ganin takardar sakamakon zaɓen na fidda gwani.

KU KUMA KARANTA:An yi jana’izar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu

“Sun fusata ne suka buƙaci jami’in zaɓe ya ba su takardar sakamakon zaɓen sai kuwa ya ce ta na wajen Ajaka.

“Don haka suka yi masa duka a wurin, inda kuma garinsu ne. Jama’a sun fusata sosai da lamarin, inda rigimar ta ƙare a wajen.”

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Dakta Ajaka ya ce an zarge shi ne da riƙe takardar sakamakon zaɓen.

Ya yi bayanin cewa a lokacin da yake ƙoƙarin bayyana kansa, ’yan daban sun auka masa inda suka yi masa mugun duka.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like