Dokta Wailare Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Zuwa PDP Tare da Magoya Baya Sama Da Dubu 10

0
513

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

FITACCEN dan siyasar nan dake mazabar tarayya ta Dambatta da Makoda Dokta Saleh Musa Wailare ya fice daga jam’iyyar APC Kuma ya koma jam’iyyar PDP tare da magoya bayan sa fiye da mutane dubu 10 maza da mata.

Dokta Wailare, wanda ya kasance daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar ta APC a yankin kananan hukumomin Dambatta da Makoda, ya bada gagarumar gudummawa sa wajen bunkasa Jam’iyyar APC a wannan mazaba da Jihar Kano da Kuma kasa baki daya.

Da yake ayyana ficewar tasa daga Jam’iyyar ta APC, Dokta Wailare ya bada dalilan sa na barin Jam’iyyar ta APC da cewa Uwar jam’iyyar ta Jihar ba ta yin komai da bangaren sa duk da irin kokarin da ya yi na bunkasa Jam’iyyar da Kuma rike magoya bayan Jam’iyyar tun lokaci mai tsawo.

Haka kuma a cikin wasikar da ya gabatarwa shugaban Jam’iyyar APC na mazabar Wailare, Dokta Saleh Musa Wailare ya sanar da cewa ya yanke shawarar ficewa daga Jam’iyyar ne saboda rashin yin duk wasu harkoki da shi da magoya bayansa na siyasa, don haka ne ya zabi barin Jam’iyyar da komawa Jam’iyyar PDP domin ci gaba da harkokin sa na siyasa.

Idan dai za a iya tunawa, matasan yankin Dambatta da Makoda sune suka saya masa takardar neman tsayawa takarar zama dan majalisa domin wakiltar kananan hukumomin Dambatta da Makoda a majalisar wakilai ta tarayya duba da yadda al’ummar wannan mazaba suke bukatar sa da ya yi.

A halin yanzu dai Dokta Saleh Musa Wailare ya amsa kiraye-kirayen da al’ummar wannan yanki suka yi ta yi na ya koma Jam’iyyar PDP domin yin takarar wakilcin mazabar Dambatta da Makoda a babban zaben da za a gudanar na shekara ta 2023, inda yanzu haka magoya bayan sa suna ta murnar wannan amsa Kira da ya yi na tsayawa takarar a inuwar jam’iyyar ta PDP.

Leave a Reply