An Soke Taron Shugabannin Zartaswan APC Na Kasa A Ranar Alhamis

0
444

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

KAMAR yadda wata sanarwar da ta fito mai dauke da sa hannun sakataren babban kwamitin rikon Jam’iyyar APC kuma sakataren kwamitin shirya zaben shugabannin na kasa Sanata Dokta John James Akpanudoedehe da mai magana da yawun Jam’iyyar APC Alhaji Salisu Na’inna Dan batta, ta bayyana cewa an soke taron shugabancin Zartaswan Jam’iyyar da aka shirya yi.

Takardar wacce ke kunshe da bayanin umarnin shugaban kwamitin rikon Jam’iyyar APC na kasa kuma shugaban babban kwamitin shirya zaben shigabanni na kasa Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ta bayyana cewa in sanar da soke taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da aka shirya yi a matakin kasa a ranar Alhamis 17 ga watan Maris 2022 don haka an soke wannan taro.

Leave a Reply